Connect with us

Uncategorized

Hukumar ‘Yan Sandan Najeriya ta sanar da ranar Jarabawa ga masu neman aikin tsaro

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hukumar Jami’an tsaron Najeriya ta gabatar da ranar da zasu gudanar da jarabawa ga masu neman aikin tsaro 210,150 da aka gayyata ga jarabtan shiga aiki a hukumar a shekara ta 2019.

Hukumar ta sanar da ranar 1 ga watan Yuli, 2019, don kadamar da jarabawa ga masu neman aikin tsaro da aka gayyata, don fid da wadanda suka dace da cin nasarar jarabawan shiga aikin tsaron.

Naija News Hausa ta sami tabbacin cewa za a yi wannan jarabawan ne a dukan jihohi 36 na kasar Najeriya, har da birnin Tarayya, FCT, daga ranar 1 ga watan Yuli zuwa ranar 28 ga watan Yuli 2019.

Hukumar ta sanar da hakan ne a ranar Laraba da ta gabata a bakin kakakin yada yawun hukumar tsaron, PSC Ikechukwu Ani, wanda ya bayyana da cewa sun riga sun sanar da wadanda zasu yi jarabawan.

Bisa bayanin Ani, ya fada da cewa bisa fom da aka cika a wata Janairu, hukumar ta karbi cikon fom 315,032 daga masu neman aikin tsaro a kasar. Ya kuma bayar da cewa Jihar Neja ne ke da yawar shigar da fom na mutane 12,247, sa’anan kuma Jihar Legas na da kankanin shigar fom na mutane 1,305.

“Hukumar mu ta karbi shigar fom daga Maza 182,926, Mata kuma da yawar 27,224” inji PSC Ani.

KARANTA WANNAN KUMA; Bayanin shugaban Majalisar Dattijai, Lawan ya fada game da Albashin ‘yan Majalisai