Uncategorized
Harsashin Bindiga ya kashe wata yarin a Fada tsakanin ‘Yan Sanda da Sojoji a Maiduguri
Naija News Hausa ta karbi rahoton mutuwar wata karamar yarinya mai shekaru 7 ga haifufwa, da aka kashe da watsin harsashen bindiga a wata fada da ya tashi tsakanin ‘yan sanda da sojoji a shiyar su.
Yarinyar da aka gane sunanta da Janada Yamta, mai shekaru 7 ga haifuwa ta kai ga karshen rayuwarta ne bayan da hukumomin tsaro biyun suka shika farmaki da junansu.
Mugun fadar ya faru ne a Maiduguri, inda harsashen bindige ya fada wa yarinyar a yayin da take barci a cikin gidan su.
Ko da shike an rutsa da ita a Asibiti amma ta karshe ga nunfashi a garin hakan.
Naija News Hausa ta fahimta da cewa fadar ya tashi ne ranar Lahadi, 23 ga watan Yuni, 2019 a yayin da wani Soja da bai sanya kakinsa ba yake kokarin shiga wani wuri inda ake faka Tireloli don ya shiga shan kayan Maye.
‘Yan Sandan da ke bakin kofar shiga wajen sun yi kokarin katange shi, daga nan sai gardama da jayayya ya tashi tsakanin su.
“Anan take aka harbe wani Ofisan ‘yan sanda, Sergeant Usman tare da wasu mutane biyu”
“Garin harbe harben ne harsashin bindiga ya iske yarinyar a cikin gidansu” inji mai bada bayani ga manema labarai.
Kalli wannan Bidiyo a kasa;