Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Jumma’a, 28 ga Watan Yuni, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Jumma’a, 28 ga Watan Yuni, 2019

1. Shugaba Buhari ya rantsar da Ciyaman na Hukumar RMAFC

A ranar Alhamis da ta gabata, Shugaba Muhammadu Buhari ya rantsar da Mista Elias Mbam, a matsayin ciyaman na Hukumar Karba da tsarafar da Ravanu ta kasa (RMAFC).

Shugaban ya kuma rantsar da Kwamishanoni 30 ga hukumar, a ganewar Naija News Hausa.

2. Shugaba Buhari ya bayyana lokacin da za a fara biyan kankanin Albashin Ma’aikata

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Alhamis da ta wuce, ya bada haske ga gurin gwamnatinsa wajen tabbatar da fara biyan sabon tsarin kankanin albashin ma’aikata na dubu talatin (30,000), kamar yadda aka amince da ita a baya.

Shugaban ya kuma gargadi gwamnonin Jiha da jiha hade da shugabannan kamfanoni da tabbatar da adalci wajen biyan albashin da ya dace ga ma’aikatansu.

3. Ba dole bane sai Dalibi yayi hidimar Bautan kasa (NYSC) kamin ya shiga takaran Gwamna – Kotu ta fadi haka

Kotun Koli ta birnin Tarayyar Najeriya (FCT) ta nuna watsi da zancen cewa duk dalibin da ya kamala karatun jami’a da kuma bai je hidimar bautar kasa (NYSC) bai da damar shiga takara da neman kujerar gwamna.

Kotun ta furta hakan ne bisa wata karar zargi da aka gabatar a gaban kotun akan Gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun, daga hannun tsohon Sanata, Iyabo Anisulowo.

4. Kotun Kara ta yi watsi da rubutacciyar ƙara game da Buhari

A ranar Labara da ta gabata, kotun hukunci ga karar zaben kasar Najeriya ta gabatar da yin watsi da wata rubutacciyar ƙara da aka mika a gaban kotun, na neman janyewar Jam’iyyar Hope Democratic Party (HDP) daga zancen kalubalantar shugaba Muhammadu Buhari ga zaben 2019.

Naija News Hausa ta gane da hakan ne bisa bayanin Alkali Mohammed Garba, a yayin da yake gabatarwa game da karar zaben shugaban kasa ta 23 ga watan Fabrairu da ta gabata.

5. Amaechi ya tada murya ga bayyana masu kokarin lalatar da adalcinsa

Tsohon Ministan harkokin sufuri, Hon. Rotimi Amaechi, ya gabatar da zargin cewa wasu na neman bata masa suna a kasar.

A wata sanarwa da aka bayar ga Naija News a ranar Alhamis da ta gabata daga hannun rukunin sadar da labarai ga Amaechi, ya bayyana da cewa kokarin ‘yan neman shugabanci kotayaya na kokarin su lalatar da sunansa da kuma adalcinsa.

6. Kotu ta daga ranar Hukunci ga Karar da aka gabatar game da Ganduje

Alkali Ahmed Tijjani Badamosi da ke a Kotun Koli ta Jihar Kano, ya dagarda hukuncin karar da masu nadin sarautan Jihar Kano suka gabatar a kotun akan matakin Gwamna Abdullahi Ganduje na kara sabbin kujerar sarauta hudu ga Jihar a baya.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Gwamnan Kano ya kara kujerar Sarauta Hudu a Jihar Kano.

7. Shugabanci kasar Najeriya na shirin sanya sabbin Ministoci

Hukumomin Tsaron kasar Najeriya sun fara shirin bada sunayan wadanda zasu yi rikon kujerar Minista a hukumomin daga Jihohi daban daban.

Naija News ta fahimta da cewa an fara wannan shiri ne kamin shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da masu jagoranci a rukunin shugabancin sa ta karo biyu.

8. Dalilin da yasa Buhari ba zai iya bayar da shugabanci ga Tinubu ba – Adebanjo

Shugaban Hadadiyar Kungiyar Zamantakewar Al’adar Yarbawa da aka fi sani da Afenifere, Mista Ayo Adebanjo ya kalubalanci shugaban tarayyar Jam’iyyar APC, Bola Tinubu da wasu manya daga Yarbawan kasar da yaudarar shugaba Muhammadu Buhari a diban cewa suna murna da shugabancin sa.

“Suna yaudaran shugaban ne don don watakila zai bayar da daman neman shugabancin kasar ga Kudu maso yammacin kasar a shekarar 2023.

9. Ka bada shaidar cewa na sace Motoci 67  – Okorocha ya kalubalanci Ihedioha

Tsohon Gwamnan Jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha ya kalubalanci sabon gwamnan Jihar da ya maye gurbinsa, Emeka Ihedioha da cewa ya bayyanar da shaidan tabbacin zargin da yake a gareshi na sace motocin jihar guda 67.

Okorocha ya kuma bada tsawon kwanaki bakwai ga Ihedioha don gabatar da shaidarsa akan zargin.

Ka samu kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com