Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litini, 1 ga Watan Yuli, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litini, 1 ga Watan Yuli, 2019

1. An Sanya Shugaban kasar Niger a matsayin Ciyaman na ECOWAS

Manyan da jigo a hukumar ECOWAS sun zabi Shugaban kasar Niger, Issoufou Mahamadou a matsayin Ciyaman na hukumar ECOWAS.

Naija News ta gane da cewa shugaba Issoufou Mahamadou zai jagoranci hukumar ne a tsawon shekara daya.

2. Saraki ya tona asirin shugaban EFCC, Magu

Tsohon shugaba da jagoran Sanatocin Najeriya, Bukola Saraki ya gabatar da wasu asiri da zargi ga Ciyaman na Hukumar kare Tattalin Arziki da Yaki da Cin Hanci da Rashawan Najeriya (EFCC), Ibrahim Magu.

Saraki ya bayyana da cewa a baya a shekarar 2016, Ciyaman na Hukumar EFCC ya ziyarce shi da rokon cewa ya taimaka masa da ganin cewa an sake zaben shi a matsayin shugaban Hukumar.

3. Atiku ya gabatar da karar Biliyan N2.5bn ga ma’aikacin shugaba Buhari

Dan takaran kujerar shugaban kasa a zaben 2019 daga Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya gabatar da sabon karar biyan kudi naira biliyan N2.5bn ga Lauretta Onochie, wadda ke wakilcin shugaba Muhammadu Buhari a layin sadarwa ta yanar gizo.

Naija News ta fahimta da cewa Atiku ya yi karar Onochie ne akan zargin shi da tayi a baya ranar 7 ga Mayu 2019, da cewa sunan Atiku na cikin jerin sunayan da hukumar tsaron kasar Arab ke nema da kamu.

4. APC sun mayar da martani ga jita-jita fada da shugabanci Buhari

Jam’iyyar shugabancin kasa, APC sun bayyana watsi da jita-jitan da ake yawo da ita na cewa Jam’iyyar nada rashin ganewa da shugabancin shugaba Muhammadu Buhari akan jinkirta da gabatar da rukunin shugabancin sa ta karo biyu.

Naija News ta gane da cewa Jam’iyyar Dimokradiyya, PDP ne suka gabatar da zargin cewa APC na da rashin amincewa da shugabanci Buhari.

5. Mutane Biyu sun mu, wasu kuma sun bace a hadarin jirgin Ruwa a Legas

Wata hadarin Jirgin Ruwa da ta auku a Jihar Legas ya tafi da rayukan mutane biyu, a yayin da kuma wasu mutane suka fada a ruwa da bacewa.

Bisa rahotannai, Naija News ta fahimta cewa jirgin ruwan na dauke ne da fasinjoji 20 da ya dauko daga Badore a shiyar Ajah enroute Egbin jetty, Ijede ta Ikorodu, ranar Asabar da ta wuce.

6. Kasar Madagascar sun ci nasara ga ‘yan kwallon kafa ta Super Eagles

‘Yan wasan kwallon kafar kasar Madagascar sun lashe ragar ‘yan wasan kwallon Najierya (Super Eagles) da gwalagwalai 2:0, a wasar kwallon Hadayyar Afrika da ake kira (Africa Cup of Nations -AFCON).

Hakan ya faru ne a ganawar wasar da ‘yan kwallon Najeriya suka yi da ta Madagascar a ranar Lahadi da ta gabata.

7. Shugabanci Najeriya ta bayyana abin alkhairi da kasa zata samu wajen kafa Ruga

Naija News Hausa ta gane da cewa gwamnatin Tarayya ta dage ga zance kafa da RUGA a jihohin kasar Najeriya don amfanin makiyaya Fulani.

Gwamnatin kasar ta bayyana ga al’umar Najeriya da cewa akwai abin alkhairi da dama da kasar zata samu idan an kafa RUGA a jihohin kasar.

8. Jigo a Jam’iyyar APC yayi barazanar tona asirin Oshiomhole

Tsohon kakakin yada yawun Majalisar Jihar Edo, Hon Kabiru Adjoto yayi barazanar cewa zai tona asirin Ciyaman na hidimar neman zaben ga Jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole.

Naija News Hausa ta tuna da cewa Kotun Koli a baya ta tsige Adjoto a zaman mamban gidan Majalisar wakilan Jihar Edo, aka kuma musanya shi da Hon. Peter Akpatason.

Ka samu kari da cikakken Labaran Najeriya a Hausa.NaijaNews.Com