Connect with us

Uncategorized

Ga Dalilin da yasa Matasa suka Kone Ofishin ‘Yan Sanda a Jihar Imo

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

An bayar da dalilin da ya kawo mugun hari da matasan Irate, a Jihar Imo suka kai ga Ofishin Jami’an tsaro, harma da kone Ofishin da wuta.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa matasan Irate a jiya Talata, 1 ga watan Yuli 2019, sun rutsa wa Ofishin Jami’an tsaron Umuoke Obowo wuta. Bisa bayanin da aka bayar ga manema labarai, matasan sun gudanar da hakan ne bayan da suka fusata da ganin cewa wani Jami’in tsaron garin ya harbe dan uwansu my suna Ikenna Ogbunigwe, da bindiga har ga mutuwa.

Ko da shike an yi kokarin isar da Ogbunigwe a Asibitin Mercy ta Umuoke, amma abin takaici matashin ya mutu garin kokarin hakan.

Ganin hakan ne matasan suka fusata, suka kuma hari Ofishin Jami’an tsaron, da isarsu kuma sai suka haska wa Ofishin wuta, suka sace Makamai da kuma sakin wadanda ‘yan sandan suka sa a kulle.

Ko da shike dai ba a bayyana ko watakila an sami jami’in tsaron da aka yi wa rauni ba a harin, amma akwai fahimtar cewa DPO Ofishin ya sami tserewa da kyar.

An kuma bayana a rahoto da cewa dan sandan da ya harbe Ikenna yayi hakan ne bayan wata rashin yarjejeniya da ya tashi tsakanin shi da marigayin.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa ‘yan ta’adda sun kai hari a Ofishin Jami’an tsaron da ke a Agudama, karamar hukumar Yenagoa, Jihar Bayelsa, inda suka kashe jami’an tsaro hudu da DPO guda.