Connect with us

Labaran Najeriya

Hadaddiyar Hukumar Ma’aikata (JNPSNC) na Barazanar fara Yajin Aiki

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hadadiyar Hukumar Ma’aikatan Najeriya da hadayar kungiyoyi takwas, sun hade da barazanar fara Yajin Aiki akan jinkirtan Gwamnatin Tarayyar kasar Najeriya wajen biyan kankanin albashin ma’aikata.

Naija News Hausa ta gane da barazanar hukumar ne a wata sanarwa da aka rattaba hannu daga Ofishin Ciyaman na JNPSNC, Mista Anchaver Solomon, da kuma sakataren hukumar, Mista Alade Lawal, a ranar Litini da ta gabata. Sanarwan ya bayyana rashin amincewar hukumar da jinkirtan Gwamnatin Tarayya wajen fara biyan kankani albashin ma’aikata na naira N30,000.

Ga sanarwan kamar haka;

“A jagoranci da amincewar Hadaddiyar Kungiyar Ma’aikatan Kasa guda Takwas da ke a Jihohin Najeriya 36, ana sanar ga al’umma da cewa Kungoyin zasu kafa kai ga fara Yajin Aiki idan gwamnatin kasar ba ta dauki matakin magance jinkirta ga biyan kankanin albashin ma’aikata ta naira dubu N30,000.00 ba, kamar yadda aka amince da ita a baya”

“Tun da shike kwamitin kadamar da biyan kankanin albashin da aka nada a jagorancin shugaba Muhammadu Buhari na jinkirta da kawo wasu dalilai daban-daban ga biyan kankanin albashin ma’aikatan, kamar yadda shugaba Buhari ya amince da rattaba hannu ga biya naiara Dubu Talatin a matsayin kankanin albashin Ma’aikata, tun ranar Alhamis, 18 ga watan Afrilu 2019, mun gane da cewa gwamnatin na kokarin ne kawai ta kara dan kalilan kudi ga albashin ma’aikatan, jin kadan kuma a manta da sabon tsarin” inji sanarwan Hukumar.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya cewa Shugaban Majalisar Dattijai, Lawan yayi bayani game da Albashin da ‘yan Majalisai ke karba.

“Abin da nake so in jaddada a nan shi ne cewa ban taɓa yin imanin cewa akwai wani abu a Majalisar Dattijai da ake kira albashin Jombo (kari/boye) ba”

“A Majalisar Dokoki da Wakilai, kowa na karban daidai albashin sa ne, ni kuma ina karbar Naira Miliyan Dari Bakwai da Hamsin (N750,000) ne a matsayin albashi na.”