Connect with us

Uncategorized

Kaito! Karanta Dalilin da yasa wani ya kashe Makwabcin sa a Jihar Kwara

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Kotu Majistare ta garin Ilorin, babban Birnin Jihar Kwara, ta saka wani mutumi mai suna Umar Abubakar a gidan Maza da zargin kashe makwabcin sa Umaru Mohammed.

Naija News Hausa ta fahimta da hakan ne bayan hukuncin da Kotun ta bayar ranar Talata, 2 ga watan Yuli.

A lokacin da Ofisan ‘Yan Sanda da ke jagorancin karar, Insp. Abdullahi Sanni ke bayani game da karar a Kotu, ya bada haske da cewa an kame mutumin ne tun ranar 20 ga wata Yuni, 2019 da ta gabta da zargin kashe makwabcin sa bayan wata rashin ganewa tsakanin su.

Insfekta Sanni ya bayar ga manema labarai da cewa Abubakar ya kashe marigayin ne a yayin da suke fada don marigayin ya hana shi wasa da kanuwarsa.

“Abin ya faru ne a shiyar Banni, a karamar hukumar Kosubosu, Jihar Kwara.” inji Sanni.

“An gabatar da Abubakar a kotu ne da laifin kisa da kuma karya dokar kasa kamar yadda take a litafin dokoki, a fale ta 221 na dokar kasa”

Babban Alkali da ke wakilcin Kotun Majistare ta Ilorin, Jumoke Bamigboye, bayan da tayi binbini da zargin sai ta bada hunkuncin cewa a jefa Abubakar a gidan Jaru da ke a Okekura, garin Ilori.

A haka ta daga hukuncin karshe ga zargin da ake da Abubakar zuwa ranar 26 ga watan Yuli ta shekarar 2019.