Connect with us

Labaran Najeriya

Shugaba Muhammadu Buhari ya aika da Jerin Sunan Ministoci ga Majalisar Dokoki

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Naija News Hausa ta sami sani da tabbacin cewa shugaba Muhammadu Buhari ya aika da jerin sunayan Ministoci da zasu yi wakilci da shi a shugabancin sa ta karo biyu ga gidan Majalisar Dokoki, a yau Talata, 2 ga watan Yuli, 2019.

Ka tuna da cewa al’umar kasar, ‘yan siyasa da manyan shugabannai sunyi ta yada yawu da fadin jita-jita a baya, harma da kalubalantar shugaba Buhari da jinkirta wajen gabatar da rukunin shugabancin sa ta karo na biyu.

Bisa rahoton da manema labarai jaridar Daily Independent suka bayar, shugaba Buhari ya riga ya mikar da jerin sunayan Ministoci da zasu yi wakilci a jagorancin sa ta shekara hudu ta gaba.

Haka kazalika, Garbu Shehu, kakakin yada yawun shugaba Buhari a lamarin sadarwa, ya bayyana da cewa za a bayyanar da jerin sunayan Ministocin kamin shigewar Rana a yau Talata.

A bayanin wani, an bayyana da cewa “an riga anyi bincike da binbini akan sunayan Ministocin a jagorancin mataimakin shugaban hukumar tsaro DSS don magance samun matsala daga wata jam’iyya ko rukunin ‘yan siyasa.”

KARANTA WANNAN KUMA; Kali bidiyon yadda Mazaunan Jihar Anambra suka kori Makiyaya Fulani daga yankin su.