Connect with us

Labaran Najeriya

El-Rufai ya bada sunan Mutane 11 ga Majalisar Jihar Kaduna don tabbatar da su a zaman Ministoci

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai a yau Laraba ya gabatar da sunayen mutane goma shadaya (11) ga Majalisar Wakilan Jihar Kaduna don amince da sanya su Ministoci a Jihar.

Kakakin gidan Majalisar, Aminu Shagali ya bayyana sunayan mutanen da El-Rufai ya bayar a Majalisar..

Ga sunayan da kuma shafen da zasu wakilta a Jihar;

1- Ja’afaru Sani               –      Ministan Harkokin Kananan Hukumomi

2- Idris Nyam                  –      Ministarn Kasuwanci, Fasaha da Tsarafarwa

3- Shehu Muhammad     –      Ministan Ilimi

4- Husaini Garba             –      Ministan kula da Albarkatun Halitta

5- Kabiru Mato                –      Ministan Karfafa Wasannai

6- Balaraba Aliyu-Inuwa   –     Ministan Ayuka da Kadamarwa ga Jama’a

7- Samuel Aruwan            –     Ministan Tsaron Ciki da harkokin Gida

8- Fausat Ibikunle             –     Ministan Gidaje da ci gaban birane

9- Muhammad Saidu        –     Ministan sha’anin Kuɗi

10- Hafsat Bello                –      Ministan Ayyukan Al’uma da ci gaban zamantakewa

11- Aisha Dikko                –       Ministan Kwamishanan Alkalai

Hon. Samuel Ubankato ya bukaci mutane 11 da Gwamnan ya gabatar da su halarci gaban Majalisar don yi masu bincike mai kyau a ranar Alhamis, 4 ga watan Yuli 2019 a gidan Majalisar .

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya aika da Jerin Sunan Ministoci ga Majalisar Dokoki.

Ko da shike a Manyan Labaran Jaridun Najeriya ta yau, shugaba Muhammadu Buhari ya karye batun da cewa lallai bai mikar da sunayan ga Majalisar Jihar ba tukuna.