Connect with us

Uncategorized

Gobarar Motar Tanki ya tafi da rayuka akallA 37 da barin mutane 101 da Raunuka a Benue

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Akalla mutane 37 suka mutu a wata hadarin motar tanki da ya auku a ranar Talata, 2 ga watan Yuli 2019 da ta gabata a Jihar Benue.

Naija News Hausa ta fahimta cewa hadarin Motar Tankin da ya faru a ranar Talata, a shiyar kauyan Ahumbe, yankin Makurdi-Aliade-Otukpo, a karamar Hukumar Gwer, Jihar Benue, ya tafi da yawar rayuka 37 da barin tulin mutane da mugun raunuka.

Bisa rahoton da aka bayar ga manema labarai, an bayyana da cewa kimanin mutane 101 ne suka sami mugun rauni kuma an haura da su zuwa asibitoci daban daban don basu kulawa.

Bincike ya nuna da cewa mugun yanayin ya faru ne a misalin karfe 2:30 na tsakar rana, a ranar Talata, 2 ga watan Yuli a yayin da Motar Tanki da ke dauke da mai a ciki ta fashe da wuta a Ahumbe.

Kwamandan Hukumar (FRSC) ta Jihar Benue, Aliyu Baba, ya bayyana ga manema labarai a Makurdi ranar Talata da ta wuce, da cewa ba mamaki a samu kari ga yawar mutane da zasu mutu a yayin da wasu da ake bawa kulawa a asibitocin ke cikin mawuyacin hali wanda ba tabbacin cewa zasu rayu saboda irin hali da suke ciki.

Dangin daya daga cikin mutanen da ake bawa kulawa a asibitin, Godwin Ayange ya fada da cewa “kan na mai shekaru 18 ga haifuwa, Paul na dawowa ne daga makaranta bayan da suka tashi karfe biyu na rana a lokacin da hadarin motar ya faru” inji Godwin.

“gobarar wutan ya tashi da motar tankin ne a yayin da karfen wata motar Bus ya tsaga kan hanya a guje, a hakan ne wuta ya kyasta sanadiyar karfen motar da ya tsage kan titi.  bus that was maneuvering its way used its exhaust to scratch the road and that sparked the fire which burnt many people including my brother” inji Godwin.

KARANTA WANNAN KUMA; Dalilin da yasa Matasa suka Kone Ofishin ‘Yan Sanda a Jihar Imo