Connect with us

Uncategorized

Kalli Bidiyon yadda Sanata Elisha Abbo ya kwakwada wa wata mata Mari a Abuja

Published

on

at

An gabatar da bidiyon yadda Sanata Elisha Abbo, Sanatan da ke wakilci a Arewacin Jihar Adamawa a karkashin Jam’iyyar Dimokradiyya (PDP) ya zalunci wata Macce da kwakwada mata mari wata shagon, inda ake sayar da kayan yin Jima’i a birnin Abuja.

Naija News Hausa ta gane da cewa Sanata Abbo ne sanata mai kanancin shekaru a cikin Sanatocin Najeriya.

A cikin bidiyon, a nino Yadda sanatan ke cin zaluncin Matar da bugun ta a cikin shagon. Ko da shike kaga yadda ake rokon sanatan da yayi hakuri, amma bai kula da hakan na, sai kwakwada mata mari yake yi a gaban mai shagon da kuma jami’an tsaro da ke biye da shi.

Ba a gane sanadiyar hakan ba, amma Sanatan a wata Rahoton da aka bayar a shafin Naija News na turanci, Sanata Abbo ya bayyana da kuma amince da cewa lallai shi ne ke a cikin bidiyon.

Ko da shike Abbo ya gabatar da cewa lallai an yanke wata shafin Bidiyon, da cewa akwai shafin bidiyon inda kanuwarsa ta fadi a kasa ta kuma suma. Sanatan bai bada haske ga sanadiyar faduwar kanwarshi ba amma ya iya nuna da cewa akwai dalilin da yasa yayi hakan.

Ya kuma fada a cewa lallai shi ba sanata bane a lokacin da abin ya faru, da cewa abin ya faru ne tun kwanakin baya kamin ya lashe kujerar zama sanata.

Ko da shike kuma an sanar da cewa abin ya faru ne tun ranar 11 ga watan Mayu da ta wuce, watau wata daya kamin aka rantsar da shi a matsayin Sanata a kasar.

Kalli Bidiyon a kasa;Advertisement
close button