Connect with us

Uncategorized

PDP: Ga bayanin Atiku game da Laifin Sanata Elisha Abbo

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana bacin ransa da halin zalunci da Sanatan da ke wakilcin Arewacin Jihar Adamawa, Sanata Elisha Abbo ya aikata.

Atiku yayi kira da bukatar Sanata Abbo da yaje a fili ya roki matar da ya yiwa duka a birnin Abuja cikin wata shago inda ake sayar da kayan jindadin jima’i, ya kuma bukace da mikar da kansa ga hukuma.

Ka tuna mun sanar da bada wata bidiyon yadda Sanatan ya zalunci wata mata a birnin Abuja akan laifin da ba wanda ya san da shi.
A halin yanzu, bidiyon ya riga ya mamaye layin yanar gizo a yayin da ‘yan Najeriya ke ta yada yawu da zagin Sanatan.

Dan takaran kujerar shugaban kasa a zaben 2019 daga Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar a yau Laraba, ya bayyana da cewa yaci karo da bidiyon kuma abin ya zan da takaici, abin bacin rai da haushi, inji fadin sa.

“Kwarai da gaske na san Sanata Abbo da kyau, amma dole ne abi doka, dole ne kuwa shugaba ya nuna kansa a matsayin shugaba” inji Atiku.

Kalli Sakon Atiku a layin Twitter;

“Na shawarci Abbo da ya fita a fili don rokon matar da yayi wa duka, da kuma mikar da kansa ga jami’an tsaro don  nuna kansa a matsayin matashi da ya isa jagoranci da kuma ya san doka. Ina kuma kira ga Jam’iyyar mu PDP da tabbatar da cewa ta dauki mataki ta musanman wajen hukunta Elisha Abbo a kan doka.”