Labaran Najeriya
Ga sabuwa: Shugaba Buhari ya dakatar da zancen kafa RUGA a Jihohin Kasar Najeriya
Gwamnatin Tarayyar Najeriya a jagorancin shugaba Muhammadu Buhari ta janye da dakatar da shirin kafa #RUGA a Jihohin kasar kamar yadda aka gabatar a baya a rahotannai.
Naija News Hausa ta fahimta da cewa shugaba Buhari ya dauki wannan matakin dakatar da kafa #RUGA ne bayan da al’umar Najeriya suka bayyana rashin amincewarsu da hidimar.
Ka tuna a baya da cewa Kungiyar zamantakewa da ci gaban Al’umma Iyamirai da aka fi sani da Ohanaeze Ndigbo, sun dage da cewa ba zasu bayar da fili ga makiyaya Fulani ba don kiwo a Kudu maso gabashin kasar.
Haka kazalika mazaunan yankin Nnewi, a Jihar Anambra suka kori wasu makiyaya Fulani daga garin su a tsakar rana, a cikin wata bidiyo da Naija News Hausa ta ci karo da shi a layin yanar gizon nishadi.
Cikakken bayani game da matakin shugaba Buhari a kan dakatar da kafa #RUGA zai biyo daga baya.