Uncategorized
Gbajabiamila ya gabatar da sabon jagoran babban Rukunin Majalisar Wakilai
Kakakin yada yawun Majalisar Wakilai, Hon Femi Gbajabiamila ya gabatar da Ado Doguwa, dan majalisa da ke wakilcin Jihar Kano a karkashin Jam’iyyar APC, a matsayin jagoran babban rukunin Majalisar wakilai.
Naija News Hausa ta gane da hakan ne a sanarwan da Gbajabiamila ya bayar a yau Alhamis, 4 ga watan Yuli, anan birnin Abuja.
Haka kazalika aka gabatar da Mista Peter Akpatason, dan Majalisa daga Jihar Edo a karkashin Jam’iyyar APC, a matsayin mataimakin jagoran Majalisar.
Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya gabatar da sunayen mutane goma shadaya (11) ga Majalisar Wakilan Jihar Kaduna don amince da sanya su a kujerar Ministoci a Jihar.
Kakakin gidan Majalisar, Aminu Shagali ya bayyana sunayan mutanen da El-Rufai ya bayar a Majalisar.
KARANTA WANNAN KUMA; Tasirai da ke cikin ga Anfani da Namijin Goro da baka san da su ba.