Connect with us

Uncategorized

Hukumar ‘Yan Sandan Kebbi sun kame mutane shidda da zargin Fyaden Dole

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hukumar Jami’an Tsaron ‘yan sandan Jihar Kebbi, sun kama mutane shida da ake zargi yi wa ‘yan mata biyu da wata Matan Aure fyaden dole a shiyar Warra, nan karamar hukumar Ngaski ta Jihar.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Alhaji Garba Danjuma, ya sanar da zancen ga manema labarai a Birnin Kebbi ranar Laraba da ta gabata.

Ya bayyana da cewa “Ranar 22 da watan Mayu ta shekaran 2019, rukunin ‘yan sanda da ke a Warra sun kama wani mutumi mai suna Usman Lawal tare da wasu biyu, duk daga garin Baka, a karamar hukumar Ngaski da zargin fyaden dole”

“Sun hari wata Matan Aure mai suna Safiya Audi da Adduna a hannun su, sun kuma sace Naira dubu N92,250 daga hannunta bayan da suka yi mata Fyaden dole”

“‘Yan sanda sun kama mutane uku daga cikin wadanda ake tuhumar su da aikata laifin, kuma sun sake gano wasu makamai da kayan doka a garesu, bayan da suka furta da amince cewa sun aikata laifin”

Danjumma ya kara da bayyana cewa sun kame Badamasi Mamuda mai shekaru 25, da Yahuza Aliyu, mai shekaru 23 tare da Anas Abubakar, mai shekarar haifufwa 20, a ranar 10 ga watan Yuni da ta gabata a garin Warra, da zargin yiwa Fatima Ibrahim ‘yar shekara 13 da Shafa’atu Sani, mai shekaru 13 ita ma fyaden Dole.“

Haka kuma aka gane da cewa sun sace Akuyoyi 29 da Shanu 2 a harin.

Bis bincike, ana tuhumar su Ukun da kasance cikin masu sace-sace dabobbin mutane a tsakanin ma hadin kasar Najeriya da ta kasar Nijar, daga  shiyar karamar hukumar Arewa a Jihar Kebbi”

Jami’in Tsaron ya bayyana da cewa su Uku sun rigaya da amince da aikata laifin, “za a tafi da su a Kotu don hukunta su a kan dokar kasa” inji Jami’in tsaron.

KARANTA WANNAN KUMA; Dalilin da yasa Matasa suka Kone Ofishin ‘Yan Sanda a Jihar Imo