Connect with us

Labaran Najeriya

APC/Buhari: Atiku da PDP zasu fara gabatar da shaidu a yau gaban Kotu

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Jam’iyyar Dimokradiyya (PDP) da dan takaran su ga kujerar shugaban kasa a zaben 2019, Alhaji Atiku Abubakar zasu fara gabatar a gaban Kotun Kara a yau da shaidun tabbacin ainihin sakamakon zaben shugaban kasa ta watan Fabrairun da ta gabata.

Naija News Hausa ta tuna da cewa Atiku da Jam’iyyar Adawa sun gabatar da jerin shaidu 400 don karyace nasarar Buhari, dan takaran shugaban kasa a karkashin jam’iyyar APC a zaben 2019.

Makon da ta gabata, Atiku da rukunin sa sun gabatar da shaidu dubu bisa dubu daga jihohi 10 a kasar don bada tabbacin su ga zargi da rashin amincewa da sakamakon kuri’un shugaban kasa ta ranar 23 ga watan Fabrairu, wadda ya bayyana shugaba Muhammadu Buhari a matsayin mai nasara ga zaben.

Jihohin da PDP suka gabatar da shaidun su na kamar haka; Jihar Niger, Yobe, Katsina, Kebbi, Borno, Jigawa, Gombe, Bauchi, Kaduna da kuma a Jihar Kano.

Bayanai game da zaman kotun a yau zai biyo daga baya….