Connect with us

Uncategorized

Wata ‘Yar Shekara 19 ta kashe Yayanta a Jihar Kano akan gardama

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Jami’an tsaron Jihar Kano sun gabatar da kame wata ‘yar karamar yarinya da zargin kashe dan uwanta da yuka.

Naija News Hausa ta karbin rahoton cewa ‘yan sanda sun kame ‘yar shekara goma sha tarar ne, mai suna Mariya Sulaiman, da zargin kashe yayan ta, Sani Sulaiman, mai shekarun haifuwa 30.

Bisa bayanin da aka bayar ga manema labarai, Mariya da Sani, tare sun sami rashin ganewa ne akan wata hidimar liyafa da suka shirya wa ‘yar uwansu da ke da aure a ranar Asabar da ta gabata a Badawa quarters, nan karamar hukumar Nassarawa, a Jihar Kano.

Don bayar da tabbacin akan lamarin, Mai bada labarai ga Jami’an tsaron Jihar, DSP Haruna Abdullahi, ya bayyana da cewa bayan da abin ya faru sun kai marigayin a asibitin Muhammad Abdullahi Wase Specialist Hospital, a inda aka bada tabbacin mutuwar sa.

An kuma bayyana da cewa an rigaya da kame Mariya, watau yarinyar da ta kashe yayanta akan hargitsi da rashin amincewa tsakanin su.

Haruna ya bayyana bisa binciken su da cewa lallai yarinyar ta kashe soke yayanta ne a hidimar, lokacin da aka sanya wata waka a zaman liyafar, “Yayan ya bukaci a canza wakar, amma Mariya ta ki amincewa da hakan, da gardaman yayi zafi kuwa, sai ta hari yayanta da wuka, anan ta kuwa soke shi a wuya, da har ta kai shi ga mutuwa”

DSP Haruna ya bayyana da cewa Kwamishanan tsaron Jihar, CP Ahmed Iliyasu, ya riga ya bada umarnin cewa a kara binciken al’amarin.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa ‘Yan Sandan Jihar Neja sun kame Matasa Uku da zargin yiwa ‘yar shekara 14 Fyaden Dole