Connect with us

Uncategorized

Karanta ka ga yadda Rundunar Sojojin Najeriya suka ribato rayuka 13 daga ‘Yan Hari da bindiga

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Rundunar Sojojin Najeriya da ke tsaro a Jihar Kaduna sun ci nasara da kashe daya daga cikin ‘yan hari da bidiga da ke damun Jihar, a ganawar wutan kuma suka iya kwato yancin mazauna 13 da maharan suka sace a yayin da suke kan aiki a gonakin su.

Bisa bayanin da aka bayar ga manema labarai, Mahara da bindigar sun sace mutanen ne a yayin da suke kan Gonakin su a yankin Kuyelo, karamar hukumar Birnin Gwari, a Jihar Kaduna, ranar Litini, 8 ga watan Yuli da ta gabata.

Jami’in tsaro da ya bayar da sanarwan ga manema labarai ya fada da cewa Sojojin sun ci nasara da hakan ne bayan da suka karbi wata kirar kula daga wata rukunin tsaron Sojojin da ke faturo a Division 1, Super Camp Kuyello, da cewa su tari mahara da bindigar a gaba, a yayin da suke biye da su da munsayar wuta.

“A yayin ganawar wutan, sojojin sun ci nasara da kashe daya daga cikin ‘yan hari da makamin, a yayin da sauran kuma suka tsere da gudu cikin dogon dajin da ke a shiyar da mumunar raunuka a jikunansu”

“a halin yanzu, darukan tsaro na zagayen nemar kama su, a yayin da ake binciken su a karkarar boda da ta bi Katsina, Zamfara da Jihar Kaduna” inji jarumin.

Ofisan da ke jagorancin Rukunin Rundunar Sojojin yankin 1 Division, GOC Major General Faruk Yahaya, ya gargadi jaruman sojojin da su kasance kullum a hake, musanman wajen taune duk wata motsin ‘yan hari da makami da suka iya gana da ita.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Bam ya tashi da Sojojin Najeriya a Chibok, lokacin da suke dawowa daga wata zagayen yaki.