Connect with us

Uncategorized

‘Yan Hisbah sun kame mutane 48 da kuma kwace katan kayan maye 37 a Jigawa

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hukumar Shari’ar Musulunci ta Jihar Jigawa, HISBAH ta sanar da kame mutane akalla 48 da kayan maye, da kuma kwace katon kayan maye 37 a karamar hukumar Taura, a jihar Jigawa.

Naija News Hausa ta gane da rahoton ne bisa wata sanarwa da Kwamandan hukumar Hisbah, Malam Ibrahim Dahiru ya bayar ga manema labarai a yau Talata, 9 ga watan Yuli a birnin Dutse.

Malam Dahiru ya bayar da cewa sun ci nasara da hakan ne bayan wata zagaye da Hukumar da ‘Yan Sandan yankin suka yi a kauyan Gugunju, a karamar hukumar Taura.

Ka tuna da cewa mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa ‘yan HISBAH sun kame Karuwai 21 da Fashe Kwalaban kayan Maye a Jigawa.

“Mun riga mun mikar da wadanda muka kama a zagayen ga ‘yan sandan yankin don kara bincike a kansu” inji Dahiru.

Ya karshe da jinjina wa mazauna shiyar, musanman matasan da ke a yankin da basu dama da kuma hadin kai wajen tafiyar da zagayen, har ga nasarar kama masu laifin a saukake.

“Muna gargadin al’uma duka da janyewa miyagun halaye da zai iya bata zamanin al’uma. Zamu kuma ci gaba da yaki da mumunar halaye kamar su shan kayan maye, karuwanci, madigo dadai sauran su” inji Dahiru.