Connect with us

Uncategorized

Mahara da Bindiga sun sace Magatakardan Jihar Adamawa

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Naija News Hausa ta karbi rahoton cewa mahara da makami sun sace babban magatakardan Jihar Adamawa.

Bisa rahoton da wani dan uwa ga wanda aka sace, ya bayar ga manema labarai da cewa an sace Mista Emmanuel ne a wata munsayar harsasu da ‘yan fashi a safiyar ranar Laraba da ta wuce a gidansa da ke a Yola, babban birnin Jihar Adamawa.

Francis Samuel, dan uwa ga Mista Emmanuel ya bayyana da cewa “mahara da bindigar sun hari gidan dan uwa na ne da ke a Clark’s Quarters, a Jimeta, misalin karfe 3:20 na safiyar ranar Laraba, suka kuma wuce da shi” inji shi.

“Sun fado ne a gidar da bindiga biyu kawai, suka kuma wuce da shi bayan kwace wayoyin salular sa da ta matar”

“Mun yi iya kokarin mu da kirar wayan mista Emmanuel amma duk a banza a yayin da ‘yan hari da makamin suka ki daukar wayar, sa’anan kuma sun ki aika da kira garemu”

A bayanin PPRO Suleiman Yahaya, ofisan yada labarai ga Jami’an tsaron yankin,  ya bayyana da cewa hukumar ta rigaya da watsar da jami’an tsaro a yankunan don neman kame wanda aka sace’