Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litini, 15 ga Watan Yuli, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litini, 15 ga Watan Yuli, 2019

1. Bulkachuwa ta hana Kotun neman yanci zuwa hutu

Shugaban Kotun neman yancin Najeriya, Alkali Zainab Bulkachuwa, ta bada umarni ga rukunin kotun da ta manta da zancen zuwa hutun da ta saba a kowace shekara a irin wannan lokacin.

Naija News ta fahimta da cewa alkalin ta gabatar da hakan ne saboda irin yawaitan kara, musanman akan hidimar zaben 2019 da kotun ke wakilci.

2. Dalilin da yasa na yiwa matar duka a Abuja – Sanata Abbo

Sanata Elisha Abbo, sanatan da ke wakilcin Arewacin Jihar Adamawa a karkashin jam’iyyar PDP, ya bayyana dalilin da yasa yayi wa wata mata duuka a birnin Abuja a cikin wata bidiyo da ya mamaye layin yanar gizo kwanaki da suka dan shige.

Ka tuna da cewa Naija News Hausa ta ruwaito da cewa Sanata Abbo, ya duki wata mata a cikin wata shago da ake sayar da kayan jima’i a birnin Abuja.

3. Iyalin Dasuki na a jire da bukatan a sake shi bisa umarnin kotu

A wata hukunci da aka bayar a boye, Alkalin kotun neman yanci ya bada umarnin cewa a saki tsohon mai bada shawarar tsaron kasar Najeriya (NSA), Col. Sambo Dasuki (rtd.), wanda gwamnatin tarayya a shugabancin Muhammadu Buhari ta saka a kulle tun shekarar 2015.

A hakan ne Iyalin Dasuki ke a jire da ganin cewa dan uwansu da ke a katangewar hukumar tsaron DSS ya samu yanci.

4. Osinbajo ya ziyarci Iyalin Pa Fasoranti

Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo a ranar Lahadi da ta gabata ya kai ziyarar ta’aziya ga iyalin shugaban Afenifere, Pa Reuben Fasoranti akan mutuwar diyar shi, Malama Funke Olakunrin da aka zargi Makiyaya Fulani da kasheta.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa an sanar da ne da mutuwar diyar shugaban kungiyar zamantakewar Yarbawa ne a ranar Jumma’a da ta wuce.

5. An kashe mutane 10 a wata sabuwar hari a Jihar Katsina

Wasu ‘Yan Fashi da makami da ba a gane da su ba a ranar Asabar da ta wuce sun kashe akalla mutane 10 da barin wasu da raunuka a shiyar kauyan Kirtawa, karamar hukumar Safana, Katsina.

An bayyana bisa rahoto da cewa ‘yan fashin sun kuma kone kimanin motoci biyar da babura a harin, bayan da suka sace shanaye.

6. Dalilin da yasa ba za a ga laifin Makiyaya Fulani ba da kashe Olakunrin – Tinubu

Shugaban Tarayyar Jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya gargadi al’ummar Najeriya da janyewa daga zargin makiyaya Fulani da mutuwar Funke Olakunrin, diyar shugaban Afenifere.

Tinubu ya fadi hakan ne a yayin da ya ziyarci gidan shugaban Afenifere a Akure, Jihar Ondo, ranar Lahadi da ta gabata.

7. An kashe Kawun Sanata Elisha Abbo, da kuma sace Maman sa

Naija News Hausa ta fahimta da cewa mahara da bindigar sun fada wa gidan Sanata Elisha Abbo, Sanatan da ke wakilcin Arewacin Jihar Adamawa, a ranar Asabar da ta wuce.

Rahoto ya bayyana da cewa an kashe Kawun Abbo da kuma sace Uwar ranan sa.

8. AFCON2019: ‘Yan wasan kwallon kafar kasar Algeria sun lashe ragar ‘yan kwallon Najeriya

A ranar Lahadi da ta gabata, ‘yan wasan kwallon kafan Algeria sun lashe ragar ‘yan wasan Super Eagles da gwalagwalai 2 da 1 a wasan AFCON ta shekarar 2019.

Wannan sakamakon wasan ya kai ‘yan kwallon Algeria ga nasar kai ga wasan karshe da Senegal da za a yi a nan gaba.

Ka samu kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com