Connect with us

Uncategorized

‘Yan Hari da Makami sun sace Maman Siasia, tsohon Kocin ‘yan wasan kwallon Najeriya

Published

on

at

Naija News Hausa ta karbi rahoton cewa ‘yan hari da bindiga sun sace Malama Beauty Ogere Siasia, Maman Mista Samson Siasia, tsohon kocin ‘yan wasan kwallon kafan Najeriya, a jihar Bayelsa.

Naija News ta kuma gane da tuna da cewa wannan itace karo na biyu da ‘yan hari da makami ke sacen maman Siasia, da aka bayyana da tsawon shekaru 76 ga haifuwa.

An sace Malama Ogere Siasia ne a watan Nuwamba ta shekarar 2015 da ta shige, aka kuma sake ta bayan tsawon kwanaki 12 da sace ta.

Bisa rahotannai da manema labarai suka gabatar, an bayyana da cewa an sace Tsohuwar ne a safiyar yau Litini, 15 ga watan Yuli.

A lokacin a Naija News Hausa ta karbi wannan rahoton, ba a samu karban bayani daga wata hukumar tsaro ba, ko kuma kila da kira daga ‘yan harin.

Labarai zasu biyo akan hakan jin kadan…

Ka tuna da cewa mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Mahara da Bindiga sun sace Magatakardan Jihar Adamawa.

Bisa rahoton da wani dan uwa ga wanda aka sace, ya bayar ga manema labarai da cewa an sace Mista Emmanuel ne a wata munsayar harsasu da ‘yan fashi a safiyar ranar Laraba da ta wuce a gidansa da ke a Yola, babban birnin Jihar Adamawa.Advertisement
close button