Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata, 16 ga Watan Yuli, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Talata, 16 ga Watan Yuli, 2019

1. Atiku da Buhari: APC da INEC sun ki amince da Jam’iyyar PDP don gabatar da wani babban shaida

Jam’iyyar APC da Hukumar INEC sun ki amincewa da matakin Jam’iyyar dimokradiyya (PDP), akan kokarin gabatar da wata babban shaida, ranar Litini ga zancen karar zaben shugaban kasa.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa alkalin da ke wakilcin shugaba Muhammadu Buhari, tare da Hukumar zabe (INEC) sun bayyana rashin amincewa da nuna shaidar.

2. Ba zamu yarda ku tsananta mu ga daukan mataki akan zaben Firamare ba – APC

Gabadin zaben kujerar gwamna a Jihar Kogi, Jam’iyyar shugabancin kasa (APC), sunyi barazanar cewa ba za su yadda da tsananci daga masu ruwa da tsaki ba a Jihar akan yadda za a gudanar da zaben Firamare.

Ka tuna cewa kwamitin kadamarwa ga Jam’iyyar sun fada a baya da cewa zasu dauki shirin kai tsaye ga zaben Firamare ta Jihar Kogi.

3. Omo-Agege ya gana da Buhari, ya bayyana Mataki na gaba kan Tsaro

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijai, Ovie Omo-Agege, ya bayyana guri da goyon bayan Majalisar Dokoki ta wajen hada kai da Rundunar Sojojin kasar, don tabbatar da kare manyan hanyoyi da ‘yan fashi da makami ke tarin mutane a koyaushe.

Omo-Agege ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga ‘yan majalisar wakilai a gida a bayan da ya kare ganawarsa da Shugaba Muhammadu Buhari a fadar Shugaban kasa, Abuja.

4. Kotu ta bada dama ga PDP don gabatar da bidiyon shaida 48 akan Buhari

Kotun kara ta amince da bukatar Jam’iyyar PDP akan gabatar da bidiyon zargi da shaida guda 48, don kalubalantar nasarar shugaba Buhari a zaben 2019.

Naija News ta fahimta da cewa PDP sun gabatar da bukatar yin hakan ne ta bakin Chris Uche, alkalin da ke wakilcin jam’iyyar ga karar kalubalantar nasarar APC da shugaba Buhari a zaben watan Fabrairu 2019 da ta gabata.

5. Abin da Miyetti Allah suka fada bayan da aka zargi makiyaya da kashe diyar Fasoranti

Kungiyar Miyetti Allah ta Najeriya (MACBAN) ta mayar da martani ga zargin laifin cewa Fulani ne suka kashe Funke Olakurin, diyar Fasoranti.

Ko da shike Miyetti Allah a cikin wata sanarwa, sun bayyana sakon ta’aziya ga Pa Reuben Fasoranti, shugaban kungiyar Afenifere, kan mutuwar ‘yarsa, Funke.

6. Obasanjo ya wallafa sabuwar wasika ga Shugaba Buhari

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ya aika da wata sako da ya wallafa a ranar Litinin, ga shugaba Muhammadu Buhari, inda yayi jawabi akan halin da yanayin da kasar ke a ciki yanzu.

A cikin sakon, Obasanjo ya yi kira da gargadin cewa a dauki matakan gaggawa wajen magance matsaloli da ake fuskanta a kasar, ya kuma gargadi masu ruwa da tsaki da su hada kai don ci gaban kasar.

7. Kungiyar Ma’aikata na barazanar shiga Yajin Aiki

Hadadiyar Kungiyar Ma’aikatan kasar Najeriya ta bukaci gwamnatin Muhammadu Buhari ta aiwatar da biyan kankanin albashin ma’ikata na naira dubu talatin (N30,000), ko kuma ta fuskanci yajin aiki daga ma’aikata gaba daya.

Kungiyar Ma’aikatan sun zargi gwamnati da jinkirta wajen biyan sabon tsarin albashi ga ma’aikatan Najeriya.

8. Dalilin da yasa sai Najeriya ta komawa yadda tsaro take a da – Atiku

Tsohon Mataimakin Shugaban kasa da kuma dan takarar Shugaban kasa na Jam’iyyar PDP ga zaben 2019, Atiku Abubakar ya yi kira ga karin matakai da zai magance rashin tsaro a Najeriya.

Atiku ya yi kirar ne a cikin wata sanarwa da aka sanya hannu da kuma aka bayar ga Naija News ranar Litinin da ta wuce.

Ka samu kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com