Connect with us

Uncategorized

Kaga Dalilin da yasa wata Mata ta zuba wa Mijinta Ruwan Zafi ga Azakarin sa

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hukumar ‘Yan sandan jihar Kano ta gabatar da kame wata matar aure, Aisha Ali, wadda ake zargi da zuba ruwan zafi a jikin maigidanta, harma ga azakarin sa.

Ofisan yada labarai da karban labaran Jami’in tsaron yankin, DSP Abdullahi Haruna, ya tabbatar da kama matar da ake tuhuma a wata sanarwa a Kano, ranar Talata da ta gabata, da laifin cin mutuncin mijinta.

DSP Haruna ya bayyana da cewa a’amarin ya faru ne a garin Feyen-Fayen a cikin karamar hukumar Danbatta.

A cikin bayanin Haruna, ya bayyana da cewa lallai hukumar ta karbi kira ne a ranar Lahadi da ta wuce daga bakin Wakilin kauyan, da cewa matar, Aisha, da aka fahimta da shekaru 35 ga haifuwa ta zuba ruwan zafi a kan Azakarin maigidanta, a nan gidan su ranar Juma’a da ta wuce.

“Mijin yana kan fama da mummunan ƙonnewar zafi a kan azzakarin sa da aka zuba ruwar zafin. An halin yanzu an kai shi ga asibitin Janara na Danbatta, inda ake bashi kulawa da ya dace” inji Haruna.

Haruna ya bada haske da cewa a bayan da hukumar su ta karbi rahoton abin da ya auku, a gurguje suka watsar da darukan tsaron Operation Puff Adder, wadda suka bi matar da kuma kameta a inda ta shiga booyo a Babura, nan a Jigawa.

Jami’in tsaron ya bayyana da cewa lallai matar, bisa bincike ta kadamar da hakan ne bayan da ta gane da cewa Mijinta na kokarin yi mata kishiya.

Haruna ya kara bada haske da cewa Kwamishanan Jami’an tsaron Jihar ya basu umarnin kama matar, da su kuma gabatar da ita a kotu bada jinkirta ba.

KARANTA WANNAN KUMA; Hukumar Makarantar Jami’a ta College of Science and Technology ta Jihar Kebbi ta kori ‘yan madigo Hudu