Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Alhamis, 18 ga Watan Yuli, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Alhamis, 18 ga Watan Yuli, 2019

1. Majalisar Dokoki ta amince da gabatar da Tanko Muhammad a matsayin CJN

A ranar Laraba da ta gabata, Majalisar Dattaija ta Najeriya sun gabatar da Tanko Muhammad a matsayin Babban shugabannan Alkalan Kotun Najeriya.

Wannan ya biyo ne bayan shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da sunan Tanko ga Majalisar don tabbatar da shi a matsayin CJN.

2. Majalisar Wakilai sunyi barazanar daukan mataki akan Gwamna Obaseki

Majalisar Wakilai ta Najeriya sun bada tsawon kwanaki bakwai ga Gwamna Godwin Obaseki, Gwamnan Jihar Edo don gabatar da wani sabon shela don kiran taron na Majalisar Jihar Edo na 9.

Majalisar Dokokin Tarayyar ta kara da cewa idan gwamnan ya kasa aiwatar da hakan a cikin lokacin da aka tsara, za su iya daukar nauyin ayyukan jihar.

3. Buhari, Lawan, Gbajabiamila sun yi wata taron daki kulle
Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Laraba da ta gabata, ya gana da Shugaban Majalisar Dattijai, Ahmed Lawan da Shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, a Fadar Shugaban kasa, Abuja.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa sun fara taron ne a misalin karfe Uku da rabi ta ranar Laraba.

4. Rukunin Gwamnatin Hukuntawa ta Najeriya ta cika da Cin Hanci da Rashawa – inji CJN Tanko

Tanko Muhammed, Babban alkalin Shari’ar Najeriya, ya bayyana da cewa gwamnatin shari’ar kasar Najeriya ta lalace da cin hanci da rashawa, kuma tana buƙatar taimakon Majalisar Dattijai.

Naija News Hausa ta gane da cewa Tanko ya bayyana wannan zancen ne a lokacin da yake amsa tambayoyin ga Sanatocin kasar lokacin da aka tabbatar da shi a matsayin Babban Alkalin Shari’ar Nijeriya a ranar Laraba.

5. Gwamnatin Jihar Edo ta bayyana sanadiyar Matsaloli da jihar ke fuskanta

Gwamnan Jihar Edo, Gwamna Godwin Obaseki ya zargi jagoran hidimar neman zaben tarayyar Jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole tare da kwamitin kadamarwan sa da alhakin matsaloli da jihar ke fuskanta.

Obaseki ya bayyana da cewa jagorancin APC da rashin cikakken binciken ta ga al’amurran ne sanadiyar matsalar da aka samu.

6. Majalisar Dattijai ta yanke shawara game da binciken Sanata Elisha Abbo

Majalisar Dattijai ta Nijeriya a ranar Laraba ta ba da karin lokaci ga kwamiti na musamman da ke bincike kan zargin da ake ga Sanata Elisha Abbo, Sanatan da ke wakilcin Arewacin jihar Adamawa.

Ka tuna a baya da cewa an gano da wata bidiyon da ya mamaye layin yanar gizo, wanda ke dauke da Sanata Abbo inda yake cin mutuncin wata Mata.

7. Kakakin Majalisar Jihar Edo ya mayar da martani ga Majalisar Wakilan Najeriya akan wata mataki

Shugaban majalisar wakilan jihar Edo, Frank Frank Okiye, ya gargadi majalisar wakilai ta Najeriya da kawar da zancen kafa bakin su ga ayyukan Majalisar jihar Edo.

Ka tuna da cewa Majalisar Wakilan Najeriya a baya ta bayar da tsawon kwana bakwai ga Gwamna Godwin Obaseki don gabatar da wani sabon shela akan taron majalisa ta 9 a Edo.

Ka sami kari da cikkaken Labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com