Connect with us

Uncategorized

Anyiwa ‘yan wasan Kwallon Niger Tonadoes alkawarin naira dubu N500,000 a kowane Gwal da suka ci Kano Pillars

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hukumar kula da kwallon kafa ta jihar Neja ta sanar da alkawarin naira dubu N500,000 na kyauta akan kowane gwal da aka zira wa ragar ‘yan kwallon Kano Pillars a karshen gasar cin kofin Aiteo 2019.

An bayyana hakan ne a bakin Shugaban kungiyar, Hon. Adamu Aliyu, a lokacin da yake bayar da kudi na Naira Miliyan Daya da Dari Biyar (N1.5 Million) da aka baiwa ‘yan wasan kafin su kammala gasar Semi-final ga cin kofin Aiteo 2019, a hadewar su da ‘yan wasan kwallon Rivers United.

A wasar Semi-final din, Niger Tornadoes ta lashe ragar Rivers United da gwalagwalai 2-1 a filin kwallon Soccer Temple, Agege a Jihar Legas.

Bisa bayanin shugaban kungiyar kulob din, ya bayyana da cewa nasarar zai samar wa kulob din kimanin Naira Miliyan daya.

“A lokacin da kuke shirin buga wasar Semi-final, hukumar tayi maku alkawarin kudi naira miliyan daya, haka kazalika Shugaban Hukumar Tsaro kuma ya maku alkawarin naira dubu dari biyar (N500,000). Ina so in tabbatar maku da cewa kudin na a nan yanzun nan. Ga wasar karshe kuma, a kowane gwal da kuka iya saka a ragar su, za a bayar da kudi rabin miliyan daya, idan kun ci kwallaye hudu, tabbas akwai Naira miliyan biyu da karin Naira miliyan daya domin lashe wasan, ma’ana, akwai Naira miliyan 3 ajiye” in ji shugaban kulob din.

A karshe shugaban kulob din ya bayyana da cewa Gwamna Abubakar Sani Bello, gwamnan Jihar Neja zai kasance a kallon wasan, “kuma ba mamaki gwamnan shi ma ya bada nashi tallafi don murnan nasara” inji shi.