Connect with us

Uncategorized

Jami’an tsaro sun kama wani da laifin soke kaninsa da Wuka har ga mutuwa

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hukumar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutumi mai shekaru haifuwa 57, da suna Tijjani Yahaya da zargin soke kaninsa da wuka har ga mutuwa.

Kakakin yada yawun Jami’an tsaron jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana da cewa marigayin, Aminu Mohammed ya mutu ne a lokacin da ake bashi kulawa a asibitin Murtala Mohammed Specialists Hospital, bayan da yayansa Tijjani ya soke shi da wuka.

A bayanin DSP Abdullahi, ya bayyana da cewa abin ya faru ne a ranar Jumma’a da ta gabata a missalin karfe 9:00 na dare, bayan da wata rashin jituwa ya auku tsakanin su Tijjani da Aminu.

Naija News Hausa bisa rahoton da aka karba ta fahimta da cewa marigayin da yayansa mazauna ne a shiyar unguwar Kofar Ruwa ta karamar hukumar Dala a Jihar Kano.

An bada haske da cewa wanda ake zargin ya soke kaninsa ne da wuka a kirjinsa a ranar 19 ga watan Yuli 2019, a misalin karfe Tara na daren ranar.

Jami’an tsaro sun gane da hakan ne bayan da suka karbi kirar kula a rukunin tsaro ta Dala Division da cewa wani mai suna Tijjani Yahaya da shekaru 57 ya soke kanin sa Aminu Mohd mai shekaru 20 ga haifuwa da wuka a kirji, a nan Makarantar Islamiyya ta Annandini Islamic school da ke a Kofar Ruwa, karamar hukumar Dala.

Jami’in tsaron ya bayyana da cewa lallai a haka, lallai an hanzarta da kai mutumin a asibiti don bashi kulawa, amma dai ya mutu a yayin hakan.

Ya kuma karshe da gabatar da cewa sun rigaya sun kame mai laifin, kuma kwamishanan tsaron jihar ya rigaya ya bayar da umarnin cewa a gabatar da karar ga rukunin hukumar da ke jagorancin halaye irin wannan.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Hukumar Tsaron Jihar Ogun sun kame Fulani Makiyaya 3 da zargin kashe wani dan shekaru 40.