Uncategorized
‘Yan Sanda sun tari ‘Yan Shi’a a sabuwar Zanga-Zanga da suka kai birnin Abuja a yau
A yau Litini, 22 ga watan Yuli 2019, ‘yan kungiyar ci gaban musuluncin Najeriya da aka fi sani da ‘yan shi’a sun fada a hannun jami’an tsaro a yayin da suka kai wata sabuwar zanga-zanga a birnin tarayyar Najeriya, Abuja a yau.
Naija News ta fahimta da cewa ‘yan kungiyar sun fada ne Abuja da zanga-zanga da kuma barazana ga Gwamnati da cewa suna a shirye don ci gaba da zanga-zanga har sai an saki shugaban kungiyar su, El-Zakzaky.
A garin hakan ne ‘yan sanda suka saki Tiya Gas da harbin Bindiga don watsar da taron zanga-zangar.
Da jin hakan sai tashin hankali ya kama matafiya da mazaunan shiyar, kowa ya wace a guje.
Kalli kadan daga cikin abin da ya auku a wannan bidiyon da ke a kasa;
Unrest in Abuja as Shiites invade Federal Secretariat, burnt NEMA emergency van. Security officials shoot tear gas to scare away protesters. #AbujaTwitterCommunity #shiites #Federalcapital #unrest #fire #burn pic.twitter.com/xPtxTpiKMO
— Oyekunle Adedamola (@Dfour4sure) July 22, 2019