Labaran Najeriya
A Karshe Shugaba Buhari ya mikar da jerin Sunayan Ministocin Next Level ga Majalisa
Bayan kimanin tsawon kwanaki 50 a Ofishi ga shugabancin kasa a karo ta biyu, Shugaban kasa Muhammadu Buhari a karshe ya mikar da jerin sunayen ministocin da zasu yi wakilci da shi a karo ta biyu ga Majalisar dattawa.
Naija News Hausa ta tuna cewa a baya majalisar dattijai ta baiwa Shugaba Muhammadu Buhari daga nan zuwa ranar Juma’a ta gaba don gabatar da jerin sunayen ministocin domin tantancewa, kamin majalisar zartarwar ta ci gaba da hutun watanni biyu na shekara da shekara kamar yadda ta saba.
Bisa ga rahoton da manema labaran The Cable suka bayar, shugaban ya mikar da jerin sunayan ministocin ne ga Majalisa da maraicen ranar Litini da ta gabata, da cewa Majalisar kuwa zasu kafa baki ga fara tantance sunayan da Buhari ya bayar a yau Talata.
Naija News ta fahimta da cewa Ministoci Goma shabiyu ne kawai za a baiwa dama daga jerin Ministoci ta da, ko da shike dai an bayyana da cewa jerin sunayan da aka bayar ya kunshi sunayan mutane 42.
KARANTA WANNAN KUMA; Hukumar ‘Yan Sandan Jihar Kano ta kama wani mutumi mai shekaru haifuwa 57, da suna Tijjani Yahaya da zargin soke kaninsa da wuka har ga mutuwa.