Connect with us

Labaran Najeriya

Kalli Jerin Sunan Ministoci da Shugaba Buhari ya gabatar ga Majalisar Dattawa

Published

on

at

Listen to article
00:00 / 00:00

Naija News Hausa ta sami tabbacin cewa shugaba Muhammadu Buhari ya mikar da sunayan Ministocin Next Level ga Majalisar Dattawa, kamar yadda muka sanar ‘yan sa’o’i da suka wuce.

Bisa ga rahoton da aka bayar da Naija News Hausa ta samu, shugaban ya sanya sunan Festus Keyamo, Babban Lauya da masu bada Shawara ga kasar Najeriya (SAN), da kuma Rauf Aregbesola, tsohon Gwamnan Jihar Osun, da kuma Godswill Akpabio, tsohon Gwamnan Jihar Akwa, dukansu cikin jerin Ministoci da Buhari ya gabatar.

A cikin jerin sunan kuma aka sami Mista Sunday Dare, Kwamishana a Kamfanin Sadarwa ta Najeriya (NCC), Sharon Ikeazor, tsohon dan Majalisar Dokoki, Tayo Alasoadura, tsohon dan Majalisar Dokokin Tarayya da kuma Olorunnibe Mamora, Tsohon kakakin yada yawun Majalisar Jihar Legas.

Ko da shike, shugaban Majalisa Dattawa, Ahmed Lawan, a halin yanzu ya riga ya fara tantance wasu sunaye daga wanda shugaba Buhari ya mika ga Majalisar.