Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata, 23 ga Watan Yuli, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Talata, 23 ga Watan Yuli, 2019

1. Gwamnatin Shugaba Buhari Ta Bayyana Abinda ke Dakatar Da Sabuwar Albashin Ma’aikata

Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari ta zargi manyan ma’aikatan gwamnati da yin jinkirta wajen aiwatar da sabon mafi karancin albashin ma’aikata da aka amince da ita a baya.

An sanar da wannan bayanin ne ta bakin Shugaban Ma’aikatan Kwadago na Tarayya, Winifred Oyo-Ita, a yayin da take zantawa da manema labarai a ranar Litinin wurin wata hidima.

2. El-Zakzaky: ‘Yan Shi’a sun kashe Babban jami’in’ yan sanda

Naija News ta ruwaito cewa membobin kungiyar Islamic Movement of Nigeria (IMN) da aka fi sani da ‘yan Shi’a sun harbe wani Kwamishina’ yan sanda (DCP), Umar Usman a birnin Abuja.

Wannan gidan yada labarai ta fahimta da cewa ‘yan Shi’ar sun harbe Mataimakin Kwamishinan‘ Yan Sanda da ke kula da Tsaron yankin ne a yayin wata zanga-zanga da ‘yan Shi’a suka yi a Abuja ranar Litinin da ta wuce.

3. IGP na ‘Yan Sanda ya dauki nauyin jagorancin karar da ke tsakanin Busola da Fatoyinbo

InSufeto Janar na ‘yan sanda, IGP Mohammed Adamu ya umarci Mataimakin Insufeto Janar na’ yan sanda (DIG) wanda ke kula da Sashen Binciken Laifi (FCID), DIG Michael Ogbizi, da ya jagoranci bincike kan zargin aikata laifin fyade da aka yi ga Fasto Biodun Fatoyinbo.

Naija News ta tuno da cewa mai daukar hoto shahararriya kuma matar mawaki, Timi Dakolo, Busola, ta zargi Fasto na Ikilisar ‘Commonwealth of Assembly Assembly’ (COZA), Fatoyinbo, da yi mata fyade shekaru 20 da suka gabata.

4. Masu zanga-zangar Shi’a da Yan Sanda sun barke da Rikici a birnin Abuja

Membobin kungiyar Islamic Movement of Nigeria (IMN), wanda aka fi sani da Shi’a sun ci karon rikici da jami’an ‘yan sandan Najeriya a yayin wata zanga-zanga a Abuja ranar Litinin.

Naija News ta fahimci cewa ‘yan Shi’ar sun gwabza fada a ranar Litinin bayan kungiyar ta kalubalanci gwamnati cewa a shirye suke su ci gaba da zanga-zangar su har sai gwamnati ta saki shugabansu, El-Zakzaky.

5. Kotun Shugaban kasa ta karyata Shaidu biyu da HDP ta gabatar akan Buhari

Jam’iyyar Hope Democratic Party (HDP) da dan takaranta ga zaben kujerar shugaban kasa a zaben 2019, Ambrose Owuru a ranar Litinin, sun bude da rufe karar da suka gabatar a gaban kotun daukaka kara kan zaben shugaban kasa.

Jam’iyyar sun gabatar da wasu takardu a matsayin shaida, amma kuma sun sami damar gabatar da shaidar mutum daya kawai yayin da kotun ta ki amince da wasu shaidu biyu.

6. Alaafin Na Oyo Ya Rubuta Wata Wasika Ga Shugaba Buhari

Alaafin Oyo, Oba Lamidi Adeyemi, a ranar Lahadin da ta gabata yayi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya gaggauta da magance matsalar kashe-kashe da satar mutane da ke addabar kasar.

Sarkin yayi kira ga hankalin shugaba Buhari game da yawan kashe-kashe da rashin tsaro da ke yaduwa a kasar, musanman harin makiyaya Fulani a kasar Yarbawa.

7. Buhari da IGP Sun gana don Tattaunawa ga Zanga Zangar ‘Yan Shi’a

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari a ranar Litinin ya gana da Insufeto Janar na ‘yan sanda (IGP) Mohammed Adamu kan rikicin da ya barke tsakanin‘ yan sanda da ‘yan Shi’a a Abuja.

Naija News ta ruwaito cewa mabiyan Shi’a da ‘yan sanda sun yi arangama a ranar Litinin bayan da kungiyar ta kalubalanci gwamnati cewa a shirye suke da cigaba da zanga-zangar tasu har sai gwamnati ta dauki matakin sakin shugabansu, Ibrahim El-Zakzaky.

8. An Gudanar da Taron Kwamitin Tsabtace Nauyin Kudin CBN A Abuja

Reshen Kwamitin Babban Bankin Najeriya sun fara wata taro na tsarin farashi na kwana biyu a ranar Litinin.

Naija News ta fahimci cewa ana duba da bukatar kwamitin da su tattauna a kan yanayin tattalin arzikin kasar, sannan da yanke hukunci game da mahimman sigogin manufofin kudi.

Ka sami kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin NaijaNewsHausa