Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Alhamis, 25 ga Watan Yuli, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Alhamis, 25 ga Watan Yuli, 2019

1. Nwajiuba ya janye daga Jam’iyyar Accord zuwa ga APC sa’o’i 24 bayan shiga jerin Ministoci

Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar EHIME MBANO / IHITE Uboma / Ubowo, Emeka Nwajiuba, wanda aka sanya sunan sa a jerin ministocin da shugaba Buhari ya bayar ga Majalisa, ya fice daga Jam’iyyar Accord zuwa Jam’iyyar APC.

An sanar da janyewar Emeka ne daga bakin Mataimakin kakakin majalisar, Ahmed Wase, a yayin da yake gabatar da da wasikar dan Majalisar.

2. Atiku ya mayar da martani ga katangewar tafiya ga kasar Amurka da aka yiwa ‘yan siyasar Najeriya

Tsohon Mataimakin Shugaban kasa kuma dan takarar Shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar PDP a zaben 2019, Atiku Abubakar ya mayar da martani ga matakin kasar Amurka na sanya dokar hana wasu ‘yan siyasar Najeriya shiga kasar US.

Wannan matakin na Atiku ya biyo ne bayan furcin da Muryar Amurka ta yi ranar Talata wanda ya la’anci matakin da wasu ‘yan siyasa suka bayyana da kawo matsala ga hidimar dimokiradiyyar Najeriya a yayin babban zaben shekarar 2019.

3. Shugaba Buhari ya rantar da Tanko Mohammed a matsayin CJN

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da Ibrahim Tanko Mohammed a matsayin Babban mai shari’a na 18 na Najeriya (CJN).

Naija News ta fahimci cewa sabon babban alkalin shari’ar ya dauki rantsuwar fara aiki ne a wani takaitaccen bikin da aka yi a cikin dakin taron shugaban kasa a Aso Rock Villa a ranar Laraba da ta gabata.

4. Jam’iyyar adawa ta janye karar su ga shugaba Buhari a Kotun Shugaban kasa

Daya daga cikin jam’iyyun adawa da ke kalubalantar nasarar shugaba Muhammadu Buhari a zaben shugaban kasa na ranar 23 ga watan Fabrairu sun janye takaddar karar da suka gabatar a kotun karar shugaban kasa.

Jam’iyyar Peoples Democratic Movement (PDM), a ranar Laraba da ta wuce, ta nemi a cire takaddinta na kalubalantar sakamakon zaben shugaban kasa na 2019 a Najeriya.

5. Majalisar dattijai ta fara tantance jerin sunayen ministocin da shugaba Buhari ya bayar

Majalisar dattiawan Najeriya a ranar Laraba, 24 ga Yuli, ta fara tantance jerin sunan mutanen da Shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar mata don tabbatar da su a matsayin ministoci a kasar Najeriya.

Kamar yadda muka sanar a Naija News Hausa a baya da cewa shugaba Buhari ya aika a jerin sunayen ministoci don tantancewa ga ‘yan majalisar dattawa.

6. EFCC ta katange dukiyar Okorocha a jihar Imo

Hukumar yaki da masu cin hanci da kare tattalin arzikin kasar Najeriya (EFCC) ta katange kofar makarantar kwalejin Rochas Foundation, wacce ke Owerri, babban birnin jihar Imo.

Naija News ta gane da cewa Jami’an hukumar EFCC sun kuma rufe makarantar Firamare da Sakandare ta Gabas, wadda ke a Owerri, da sanin cewa makarantar ta Uloma Nwosu ne, ‘yar fari ga Rochas Okorocha.

7. Gidan Majalisar Wakilai ta sake gabatar da Corps Peace, da wasu Bil 3

Majalisar Wakilai ta 9 ta sake gabatar da wasu hidima 4 da shugabancin Muhammadu Buhari taki amince da ita a gabatarwar majalisar wakilai ta 8 da suka wuce.

Hidimar na kamar haka a turance; Peace Corps, Terrorism (Prohibition and Prevention) Bill, 2019, Chartered Institute of Treasury Management (Establishment) Bill, 2019 (HB. 57); and National Commission for Refugees, Migrant and Internally Displaced Persons Bill, 2019.

8. Bai kamata Shugaba Buhari ya sanya sunan Akpabio a cikin jerin Ministocin sa ba – Sagay

Shugaban kwamitin ba da shawara ga shugaban kasa kan yaki da cin hanci da rashawa, (PACAC), Itse Sagay a ranar Laraba, ya yi Allah wadai da matakin shugaba Muhammadu Buhari ga sanya suna Godswill Akpabio a cikin jerin sunan Ministoci.

Sagay a cikin takardar da ya gabatar ya nuna cewa nadin Akpabio ya saba wa matsayin gwamnatin Buhari kan yaki da cin hanci da rashawa, a yayin da ake kan binciken tsohon Shugaban karamar rukunin Majalisar Dattawa.

Ka sami kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin NaijaNewsHausa