Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Jumma’a, 26 ga Watan Yuli, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Jumma’a, 26 ga Watan Yuli, 2019

1. Shugaba Buhari ya kai Ziyara a kasar Liberiya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tashi daga Abuja ranar juma’a zuwa Monrovia, kasar Liberia don halartar bikin cikar shekaru 172 da samun ‘yancin a kasar.

Naija News ta gane da cewa shugaba Muhammadu Buhari na daya daga cikin bako na Musamman a wajen taron, bisa sanarwan da Garba Shehu, mai taimaka masa kan harkokin yada labarai ya fada.

2. Gbajabiamila ya gabatar da Sunayen Shugabannin Kwamitin Gidan Majalisar Wakilai

Kakakin Majalisar Wakilai, Hon. Femi Gbajabiamila a ranar Alhamis ya nada shugabannin kwamitocin gidan majalisar.

Naija News ta fahimci cewa an kafa wasu kwamitoci 13, wanda ya kara adadin daga 96 zuwa 109.

3. Magu ya roki Interpol da yin sauri wajen binciken Diezani akan cin hanci da rashawa

Shugaban Hukumar Yaki da Cin hanci da rashawa da kare tattalin arzikin kasa (EFCC), Ibrahim Magu ya roki Burtaniya da ta hanzarta gudanar da bincike da kuma shari’ar tsohuwar Ministan Albarkatun Man Fetur ta Najeriya, Diezani Alison-Madueke.

Naija News ta fahimta da cewa hukumar EFCC na zargin kasar UK da jinkirta ga kadamar da hukunci ga tsohuwar ministan man fetur din da ake wa zargi na sama da shekaru hudu.

4. Macizai Sun kori ‘Yan Majalisa a Jihar Ondo

Wakilan Majalisar Dokokin Jihar Ondo sun tafi hutu marasa iyaka sakamakon mamayar macizai a inda suke zamar tattaunawar su.

Naija News Hausa ta iya gane da cewa ‘yan majalisar sun tafi hutun ne sabili da macizai da suka fado daga saman dakunan zaman ‘yan majalisar a yayin da suke cikin hidimar su a ranar Laraba da Alhamis da ta gabata.

5. INEC jihar Imo ta bayar da Takardar yancin jagoranci ga Sanata Uwajumogu

Hukumar gudanar da zaben kasa, INEC ta bayar da takardan wakilci yankin Arewacin jihar Imo ga Mista Benjamin Uwajumogu.

A ranar Alhamis a missalin karfe 4 na maraice ne aka bayar da takardan wakilcin ga Sanata Uwajumogu a hedikwatar INEC a Abuja.

6. Najeriya hau lamba 12 a kan jerin FIFA

Bayan kammala gasar cin kofin kasashen Afirka da aka yi a kasar Masar (Egypt) ‘yan kwanaki da suka gabata, Najeriya ta karu da hawa saman mataki 12 da barin lamba 45 zuwa lamba na 33 a jerin nasarar FIFA.

Naija News Hausa ta fahimta da wannan ne bisa sanarwan da hukumar FIFA ta fitar a yau, da cewa ‘yan wasan kwallon kafar Najeriya, ‘Super Eagles’ ta dage da matsayin ta a na 3 a Nahiyar.

7. Shugaban kasar Tunisiya Beji Caid Essebsi ya rasu da shekaru 92

Shugaba na farko da kuma mafi dadewa a mulkin kasar Tunisiya, Beji Caid Essebsi, ya mutu a safiyar ranar Alhamis.

Naija News ta samu labarin mutuwar Shugaban ne a wata sanarwa da aka bayar daga ofishin shugaban kasar Tunusiya da cewa Beji ya mutu.

8. Dalilin da yasa na janye daga PDP – Ngige

Tsohon Ministan kwadago, Dakta Chris Ngige, ya bayyana da cewa ya bar jam’iyyar Dimokradiyya (PDP) ne saboda ya gane da cewa Jam’iyyar bata cika da gudanarwa ta kwarai ba.

Ngige ya sanar da hakan ne ranar alhamis a yayin bayyanar sa da tantacewa ta jerin ministoci da Buhari ya bayar.

9. A karshe, Gwamnatin Iran ta bukaci Gwamnatin Tarayyar Najeriya da sakin El-Zakzaky

Babban mai gabatar da kara na Jamhuriyar Musulunci ta Iran, Mohammed Montazeri, ya yi kira ga gwamnatin tarayyar Najeriya a jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari da ta saki jagoran Harkar Musulunci ta Najeriya (IMN), Ibrahim El-Zakzaky.

A bayanin kamfanin dillancin labarai na AhlulBayt, Montazeri a wata wasika da suka wallafa a ranar Asabar din da ta gabata, ta bukaci Gwamnatin Tarayyar Najeriya da sakin El-Zakzaky don ya samu damar zuwa Iran don binciken lafiyar jikinsa.

Ka sami kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin NaijaNews.Com