Connect with us

Uncategorized

Boko Haram sun kai sabuwar hari a jihar Borno da kashe Mutane da yawa

Published

on

Mahara da bindiga a daren ranar Talata da ta gabata sun kai hari a wasu kauyukan da a yankin karamar hukumar Konduga ta jihar Borno.

Bisa ganewar NaijaNewsHausa a wata sanarwa da aka bayar ga manema labarai, ‘Yan ta’addar sun kai hari ne kauyen a misalin karfe 6:30 na yamma, a yayin da suka shigo cikin manyan motoci guda shida cike da makamai, suka kuma ci gaba da harbe-harben bindiga ko ta ina.

Naija News ta fahimta bisa rahoto da cewa ‘yan sanda da rundunar sojojin Najeriya sun rigaya da fice daga ƙauyen kwana biyu da suka gabata kamin ‘yan harin suka kai wannan sabuwar hari a kauyan.

A yayin zantawa ga manema labaran Aminiya, wani mazaunin garin, Babagana Adam, ya bayyana da cewa maharan sun isa kauyen ne a cikin motoci shida da ke cike da manyan bindigogi.

“Mun yi tunanin cewa wata kila sojojin Najeriya ne suka dawo a yakin a yayin muka gane su da shiga daya. Sai kwaram da muka ji suna ikirari da Ihun ‘Allah Alkar’, sannan kowa ya gudu daga garin, suka kuma fada a gidaje da shagunan mutane da daukar kayaki da suke so, suka kuwa tafi da su”

“Ba zani iya bayar da kimanin iya mutanen da aka kashe ba a harin, saboda mutane da dama ne suka mutu, ni kuwa in saman kan Ice a lokacin da ni ke wannan kirar”

“Haka kazalika yara kanana da ke a nan basu san inda iyayen su suka shige ba, muna bukatar taimako,” in ji Adamu.

KARANTA WANNAN KUMA; Jami’an Tsaro sun Cafke wasu Mutane biyu a Kano da zargin Kashe ‘yan Shekara Takwas