Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Alhamis, 1 ga Watan Agustai, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Alhamis, 1 ga Watan Agustai, 2019

1. ‘Yan Shi’a sun Dakatar da Zanga-zangarsu a kan El-Zakzaky

Kungiyar Harkar ci gaban Musulunci ta Najeriya (IMN), wacce aka fi sani da ‘Yan Shi’a a ranar Laraba da ta wuce ta sanar da dakatar da zanga-zanga a Abuja.

Naija News Hausa ta tuna da cewa IMN tun lokatan baya ta kafa yin zanga-zanga akan bukatar cewa a saki shugaban kungiyar su, Sheikh Ibraheem El-Zakzaky.

2. Kotun Kara ta tsige Wakilin Jam’iyyar PDP a Majalisar Dattawa da kuma musanya shi da dan Jam’iyyar APC

Kotun daukaka kara da ke zaune a Akure, babban birnin jihar Ondo ta kori Ikengboju Gboluga a matsayin memba mai wakiltar mazabar Okitipupa /Irele na mazabar tarayyar Majalisar Wakilan Jihar.

Naija News Hausa na da sanin cewa an zabi Gboluga ne a karkashin Jam’iyyar Dimokradiyya.

3. Abinda ya bata mani rai game da Apapa Gridlock – Buhari

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya sake jaddada aniyar gwamnatin sa na kara zuba jari a ci gaban kasar Najeriya.

Shugaba Buhari ya bada tabbacin ne a lokacin da ya karbi bakuncin membobin kungiyar ‘yan kasuwa da masana’antu na Legas (LCCI) a Fadar Shugaban kasa da ke Abuja ranar Laraba da ta gabata.

4. AMCON ta Saki Sunayen masu Babbar Bashi 20

Hukumar Kula da Dukiya da kayakin kasar Najeriya (AMCON) ta wallafa sunayen manyan masu bashi guda 20.

A cewar kamfanin, “masu bashi a asusun kasar” sun kai ga akalla kashi 67% na bashin Naira tiriliyan 5.

5. Atiku da Buhari: Babban jami’i ya tabbatar da sakamakon jarabawar WAEC ta shugaban kasa

Wani babban jami’in hukumar binciken hadadiyar jarabawar Afirka da ake kira (WAEC) ya tabbatar da sahihancin kwafin takardar shaidar kammala karatun jami’ar wanda Shugaba Buhari ya bayar ga Kotu a ranar Talata.

Wannan ya faru ne lokacin da jami’in, Oshindeinde Henry Adewunmi ya bayyana a ranar Laraba a gaban Kotun ta neman Shugabancin a matsayin shaida ga Shugaba Muhammadu Buhari.

6. Shugaba Buhari ya bayyana Lokacin Da Zai Sanya sabbin Ministoci a matsayin su

Shugaban kasar Najeriya, Shugaba Muhammadu Buhari ya ce zai gabatar da mukamai ga zababbun ministocinsa bayan an kamala rantsar da su.

Naija News ta fahimci cewa, Buhari ya sanar da hakan ne ta shafinsa Twitter ranar Talata, inda ya kuma yi amfani da damar wajen yabawa majalisar dattawan Najeriya saboda gagautawa wajen tantance sunayen ministocin.

7. Wata Rukuni ta Bayyana Harkar El-Zakzaky da Shi’a da zama Jabu, ta kuma gargadi Saudiyya da Iran da janye kansu

Wata kungiyar kungiyar Shi’a, Al-Thaqalayn Cultural Foundation ta bayyana Harkar Kungiyar Ci gaban Musulunci ta Najeriya a karkashin jagorancin Ibrahim El-Zakzaky a matsayin jabu.

Kungiyar ta kuma aikar da gargadi ga Jamhuriyar Musulunci ta Iran da masarautar Saudi Arabiya da su daina amfani da damar rikicin IMN don gwajin gwagwarmayar neman yankinsu.

Ka samu kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin NaijaNewsHausa