Ed-ul-Kabir: Saudiyya ta sanar da ranar 10 ga watan Agusta a matsayin ranar Arafat

Gwamnatin kasar Saudiyya ta ayyana ranar Asabar, 10 ga Agusta a matsayin Ranar Arafat, babban rana ta musanman da matafiya hajji a dukan duniya hallara a Tudun Arafat domin yin addu’o’i.

Naija News Hausa ta samu tabbacin wannan rahoton ne bisa wata sanarwa da aka fitar daga hannun Jamiu Dosunmu, na Sashin Harkokin Jama’a na Hukumar Kula da Mahajjata ta Amir-ul Hajj, Jihar Legas, Dr. AbdulHakeem Abdul-Lateef, a ranar Juma’a a Gidan Gwamnatin Jihar Legas da ke Makkah.

A bayanin sa, ya sanar da cewa Ed-ul-Kabir zai kasance ne a ranar Lahadi, 11 ga watan Agusta, 2019, lokacin da musulmai a duk fadin duniya za su sadaukar da Ragon Layya bisa doka da umarnin addinin Musulunci.