Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Jumma’a, 2 ga Watan Agusta, Shekara ta 2019

Published

on

at

advertisement

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Jumma’a, 2 ga Watan Agusta, 2019

1. Shugaba Muhammadu Buhari ya sanar da rufe karar su a Kotun Koli

Shugaban kasa Muhammadu Buhari da Jam’iyyar shugabancin kasa (APC) sun rufe kare karar su a gaban kotun daukaka kara ta Shugaban Kasa.

Naija News Hausa ta fahimta da hakan ne a sanarwan Kungiyar lauyoyi ga Buhari, karkashin jagorancin Wole Olanipekun (SAN) da kuma jagorantar lauya a jam’iyyar APC, Lateef Fagbemi, da cewa suna sanar da niyyar rufe bakin su yayin da suka gurfana a gaban kotun a ranar Alhamis.

2. An dakatar da Shugaban Karamar Hukuma Don boye ‘Yan bindiga

Majalisar Wakilai ta Jihar Zamfara ta dakatar da Ciyaman na Karamar Hukumar Maradun, Ahmad Abubakar saboda laifin raunana tsaro a Jihar.

Naija News Hausa ta gane da cewa hakan ya biyo ne bayan wata takardar karar da majalisar ta gabatar kan Shugaban karamar hukumar, wanda wasu mutane shida da ke zama a yankin suka sanar ga Majalisar Jihar.

3. Diyar El-Zakzaky ta mayar da Martani ga zancen dakatar da  Zanga-zanga

Diyar Ibraheem El-Zakzaky, shugaban kungiyar cin gaban harkan musulunci ta Najeriya (IMN) da aka fi sani da Shi’a, Suhaila Zakzaky ta dage cewa dage da cewa kungiyar ”yan shi’a za ta ci gaba da zanga-zangar ta har sai an sako mahaifinta.

Suhaila ta sanar da hakan ne a yayin da ta ke mayar da martani ga wata sanarwa daga Ibrahim Musa, shugaban kungiyar watsa labarai ga IMN da cewa, an dakatar da zanga-zangar kungiyarsu a birnin Abuja.

4. Rayuwata na cikin Hadari – Mataimakin Gwamnan Jihar Kogi, Achuba Ya sake daga muryar sa

Mataimakin gwamnan jihar Kogi, Simon Achuba ya sake tayar da murya game da barazanar da ake yiwa rayuwarsa.

Naija News ta tuno a baya da cewa Mista Achuba a farkon wannan shekarar, a watan Fabrairu ya zargi maigidan nasa da yin barazanar kashe shi. Kazalika a wata hira a ranar Alhamis da ta gabata da manema labarai a gidan sa da ke a Lokoja, Mataimakin gwamnan ya bayyana da cewa gwamna Yahaya Bello ya bada dama ga ‘yan bindiga don kashe shi.

5. Abin da kungiyar neman yanci ga Atiku suka fada bayan da Buhari da APC ta rufe kare karar sua kotu

Atiku Abubakar, dan takarar kujerar shugaban kasa a zaben 2019 daga jam’iyyar PDP ya mayar da martani ga matakin da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da shugaban kasa Muhammadu Buhari suka dauka na janye kansu daga kare karar da ake da su a Kotun shugaban kasa.

Paul Ibe, mai taimaka wa Atiku ga yada labarai a yanar gizo, ya yi amfani da shafin Twitter ranar Alhamis don bayyana ra’ayinsa game da hukuncin da APC da Buhari suka yanke.

6. An Kama wani Mutumin Saboda samar da Jabun Takaddar yancin Jagoranci da kuma Sa hannun Shugaban INEC

Rundunar Jami’an tsaro da shiyar jihar Legas ta gurfanar da wani mutum da aka sani da suna Toluwalope Akanni bisa wata zargin karkatar da takardar yancin jagoranci ta Hukumar Zabe da kuma dagewa a matsayin zama dan Majalisar Wakilai.

An zargi mutumin mai shekaru 30 da laifin samar da sanya hannu iri ta shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu.

7. Sowore na shirye don jagorar wata Zanga-Zangar Juyi

Omoyele Sowore, dan takarar shugaban kasa a zaben 2019 daga Jam’iyyar African Action Congress a babban zaben da ya gabata, ya yi kirar goyon baya ga Matasan Najeriya don kadamar da zanga-zanga.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa zanga-zangar zata kasance ne don neman juyin zamantakewa a kasar Najeriya, kamar yadda Sowore ya gabatar da cewa zanga-zangar zata kasance ne tun daga ranar 5 ga Agusta, 2019.

8. Shugabancin Kasa Ta Bayyana Dalilin da yasa Har Yanzu ba a gabatar da Rukunin shugabancin Buhari ba

Shugabancin kasar Najeriya ta bayyana cewa har yanzu majalisar dattawa ba ta yi magana da shugaban kasa Muhammadu Buhari ba akan  kammala tantance wadanda aka bayar da sunayen su ga matsayin ministoci.

Ka tuna da cewa majalisar dattijai a ranar Talata da ta wuce ta kammala gwaji da tantacewar jerin sunayen da shugaba Buhari ya mika ga Majalisar don tabbatar da nadinsu a mukamin ministocin jumhuriyyar tarayyar Najeriya.

Ka sami kari da cikakken Labaran Najeriya a NaijaNews.Com