Connect with us

Uncategorized

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litini, 5 ga Watan Agusta, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litini, 5 ga Watan Agusta, 2019

1. A karshe Hukumar DSS ta mayar da martani ga Kama Sowore Tare Da bada dalilan haka

Hukumar Tsaro da Bincike ta Jiha (DSS), a karshe ta mayar da martani da bayyana tabbacin kamun Omoyele Sowore, dan takaran kujerar shugaban kasa ga zaben 2019 da kuma mai wallafa labarai a shahararren gidan labaran yanar gizo mai suna Sahara Reporters.

Hukumar Tsaron a cikin sanarwar da ta bayar, ta bayyana da cewa sun fahimtar cewa zanga-zangar Sowore da barazanar sa zai iya tayar da kwanciyar hankali a kasar.

2. An kashe Shugaban Kungiyar Miyetti Allah a Jihar Adamawa

‘Yan hari da bindiga da ba a san da su ba sun kashe Saidu Kolaku, shugaban kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria (MACBAN) a jihar Adamawa.

Naija News Hausa ta gane da cewa maharan sun fada ne a gidan Kolaku a ranar Asabar da ta gabata, suka kuma harbe shi har ga mutuwa.

3. Obasanjo Ya gana da Hausawa/Fulani, Kudu maso Yamma tare da Shugabannin Kogi

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ya gana da shugabannin Hausa/Fulani a yankin kudu maso yamma, Kogi da kuma jihar Kwara.

Naija News ta fahimci cewa taron wanda ya Obasanjo ya wakilta a jihar Abeokuta Ogun ya kasance ne akan rashin tsaro da sace-sacen mutane a yankunan.

4. Masu Zanga-Zangar Juyin Zamantakewa sunyi barazanar ci gaba da Zanga-zangar

Kungiyar Zanga-zanga akan neman juyin mulki da zamantakewa bayyana barazanar ci gaba da zanga-zangar su a ranar Litini ɗin nan duk da cewa hukumar DSS ta kame Sowore, jagoran zanga-zangar.

Naija News ta fahimci cewa shugaban jami’an tsaron Najeriya, IGP Mohammaed Adamu ya gargadi masu zanga-zangar da barazana cewa su janye daga hakan, amma duk a banza.

5. DSS na katange mu daga ganawa da Sowore – Lauya

Shugaban kungiyar lauyoyi ta African Action Congress (AAC), Tope Akinyode, ya bayyana cewa hidimar hukumar DSS na hana kungiyar su da damar ganawa da Omoyele Sowore.

Naija News Hausa ta tuna da cewa an kama Sowore ne a safiyar ranar Asabar da ta gabata a kan zanga-zangar da ya jagoranta da kuma shirin kadamarwa a dukan fadin kasar.

6. Kada ka ba da wata sabuwar sanarwar, Kotu ta gargadi Obaseki

Wata babbar kotun kolin tarayya da ke a Fatakwal a jihar Rivers ta umarci gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo da cewa kada ya fitar da wata sabuwar wallafin sanarwar kamar yadda majalisar dattawan Najeriya suka bukace shi da hakan a baya.

Kotun ta ba da wannan umarnin ne bayan bukatar da Mataimakin Shugaban Majalisar Jihar Edo, Hon. Yekini Idiaye ya gabatar a kotun.

7. ‘Yan Sanda sun Kama ‘yan hari da makami da suka kashe Babban Firist na Katolika A Enugu

Rundunar Jami’an tsaron ‘yan sanda ta reshen jihar Enugu sun kama wasu da ake zargi da kisan wani jagoran cocin Katolika da ke a jihar Enugu, Rev Fr Paul Offu.

Naija News ta samu tabbacin hakan ne a wata sanarwa da kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Suleiman Balarabe, ya bayar a ganawarsa da manema labarai a Enugu, a ranar Asabar, 3 ga Agusta da ta gabata.

8. Boko Haram Sun kashe Mutane sama da 27,000 Tun daga shekarar 2009 – UN

Bisa wata bayanai da Majalisar Dinkin Duniya ta fitar kwanan nan, sun bayyana da cewa akalla mutane sama da 27,000 ne kungiyar ‘yan ta’adda ta Boko Haram suka kashe tun daga hare-harensu a shekarar 2009 a Najeriya.

Edward Kallon, mai ba da agaji na Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya, ya ce a kwanan nan kimanin mutane dubu 130 ne suka fice daga muhallansu, a yayin da masu ‘yan ta’addan suka kuma ci gaba da kafa sabuwar rukuni ISIS a Yammacin Afirka (ISWAP) don fatattakar da Boko Haram.

Ka samu kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin NaijaNews.Com