Connect with us

Uncategorized

Hukumar NDLEA na daukar Ma’aikata, karanta ka ga yadda zaka cika fom din a kasa

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Hukumar Hana sha da fataucin mugan magunguna ta kasa (NDLEA) ta sanar da tabbatar da cewa a yanzu haka tana daukar ma’aikata, suna kuwa yin kira ga ‘yan Najeriya da suka cancanta da su aika da sunayan su ta layin yanar gizo don neman aiki.

Sanarwan na kamar haka;

“Muna mai sanar maku da cewa muna daukar Ma’aikata a Hukumar mu a wannan lokaci”

Naija News ta gane da sanarwan ne bisa yada hukumar ta sanar da shi akan layin yanar gizon hukumar, da cewa duk mai muradin shiga aiki da hukumar ya bi layin yanar gizon su don cika Fom din.

Mun fahimta a Naija News kamar yada aka bayar a layin yanar gizon Hukumar NDLEA da cewa shigar da suna a fom din shiga aikin hukumar zai karshe ne a ranar Alhamis, 29 ga watan Agusta 2019.

An kuma gargadi masu bukatar da neman aikin da su cika fom din da hanzari. Sun kuma bayyana da cewa wanda sunan sa ya fito ga jerin sunayan da zasu fitar ne kawai zai shiga aiki da su.

Ka bi wannan layin don cika Fom na NDLEA