Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Alhamis, 8 ga Watan Agusta, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Alhamis, 8 ga Watan Agusta, 2019

1. Gwamnatin Tarayya ta canza ranar Rantsar da sabbin Ministoci

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta sanar da canza ranar da zata yi hidimar Ilimantarwa da kuma rantsar da sabin ministocin shugaba Muhammadu Buhari.

A baya kamar yadda muka sanar a Naija News Hausa, Gwamnatin Tarayya ta bayyana da hidimar ne tsakanin ranar 15 zuwa 16 ga Agusta, amma an sake sanar da sabon ranar a yanzu ga 19 ga Agusta zuwa 20 ga Agusta.

2. Jami’an Sojojin Sun Kashe Mutane Hudu Tare Da ‘Yan Sanda Uku Da Wani Mutumi a Taraba

Wasu mutanen da ake zargi da zama Sojojin Nijeriya a ranar jiya sun bude wuta kan ‘yan sanda wadanda suka kama wani shugaban ‘yan ta’adda, Alhaji Hamisu a Ibi, jihar Taraba, a yayin da ake dauke da shi zuwa Jalingo, babban birnin jihar.

An bayyana Sojojin da kashe ‘yan sanda uku, wadanda suke mambobi rukunin tsaron IG da taimakon Al’umma da tsaro.

3. Mataimakin Gwamnan Jihar Kogi na Fuskantar Tsigewa

Simon Achuba, mataimakin gwamnan jihar Kogi na kan fuskantar barazanar tsigewa a yayin da majalisar zartarwar jihar ta fara gabatar da kararaki don cire shi daga kujerar.

Hakan ya faru ne a yayin da a ranar Laraba, shugaban masu rinjayar gidan Majalisar, Abdullahi Bello ya gabatar da wasu kara.

4. Rukunin Hukumar Kwastam ta Ogun ta kasu biyu

Hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) ta yankin Jihar Ogun, ta ce ta tsarafa Kwamandan Yankin don bada damar karfafawa da yin aiki sosai a Jihar.

Daga cikin shirin, za a ƙirƙiri sabbin Yankunan Kwastam guda biyu a Jihar, ɗaya don kula da ci gaban Hukumar, gudan kuma don inganta harkar samun kudaden da ke shiga asusun hukumar.

5. #RevolutionNow: DSS har yanzu ta ki Sakin Babban Dan Jarida da ta Kama akan Labaran Facebook

Har yanzu Ma’aikatar Tsaro ta Jiha da Jiha, DSS ta dage da kin sakin wanda suka kama, watau tsohon Editan Labaran Siyasa na jaridar Daily Trust, Ibrahim Dan-Halilu.

Naija News ta fahimci cewa an kama dan jaridar ne a tun ranar Litinin din da ta gabata a Kaduna, da zargin tallafawa ayyukan RevolutionNow a shafin Facebook.

6. Shugaba Buhari Ya Gana da Shugabannin Jam’iyyar APC A birnin Abuja

Muhammadu Buhari, shugaban Najeriya a ranar Laraba, ya yi wata ganawar sirri da membobin Kwamitin Ayyuka na Kasa (NWC) ta Jam’iyyar APC.

Naija News ta fahimci cewa ganawar ta fara ne da misalin karfe 12 na rana a fadar shugaban kasa da ke Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.

7. Archbishop Martins ya Bayyanawa shuga Buhari abinda Zai Yi da Masu Zanga-zanga

‘Yan kwanaki kadan bayan da Hukumar DSS ta kama dan takarar Shugaban Kasa daga Jam’iyyar African Action Congress (AAC), Omoyele Sowore, Babban Bishof na Katolika a Legas, Mai suna Rev. Adewale Martins, ya bayyana cewa abubuwa zasu lalace idan har shugaba Muhammadu Buhari ya gaza magance matsalar rashin tsaro a kasar.

Archbishop din ya yi gargadin cewa Al’ummar Najeriya na iya daukar wannan daman don Kare kansu idan kasar ba zata iya tabbatar da tsaro ba.

8. Shugab Buhari ya mayarda martani game da tuhumar Bishof din Katolika akan Tsaro

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya mayar da martani da kalubalantar Bishop din cocin Katolika (CBCN) game da furcin da yayi da cewa zata iya jawo fargaba a tsakanin ‘yan Najeriya.

Naija News ta fahimta da cewa shugaba Buhari bai ji daɗin furci da bayanin Bishof din ba dangane da yanayin matsalar tsaro da kasar ke fuskanta.

Ka sami kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin NaijaNews.Com