Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litini, 12 ga Watan Agusta, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litini, 12 ga Watan Agusta, 2019

1. NAF ta rusa da Kangin Cibiyar Kulawa ta Boko Haram

Rundunar Sojojin ta Najeriya (NAF) ta bayyana da cewa Rukunin Darukan Tsaron ta (ATF) na Operation Lafiya Dole sun lalata wani Cibiyar Kwamandan ta ‘yan Boko Haram da ke a Dusula, daban da ta Sambisa a jihar Borno.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa rundunar ta ATF ta gudanar da wannan hari ne ta jagorancin Operation Green Sweep III wanda aka yi niyya ta musanman tarin ‘yan ta’addan da aka gano a Borno.

2. PDP ta lashe Zaben Karamar Hukumar Jihar Bayelsa

Jam’iyyar Dimokradiyya, PDP ta jihar a karshen makon da ta wuce ta lashe kujerar Ciyamomi takwas hade da kujerar Kansiloli 105 a zaben kananan hukumomi da Hukumar Zabe ta Jihar Bayelsa (BYSIEC) ta gudanar.

Naija News ta fahimci cewa PDP ta bayyana a da lashe zaben ne duk da cewa an gane da makirci da Jam’iyyar APC suka nuna a hidimar zaben jihar.

3. Kungiyar IPOB Ta yi Bayanin game da hidimar Sojojin Najeriya A Yankin Kudu Maso Gabas

Wakilan Kungiyar ‘yan asalin Biafra (IPOB) sun nuna fushinsu game da ayyukan da rundunar Sojojin Najeriya ke gudanarwa a yankin Kudu Maso Gabashin kasar, musamman a jihar Abia.

Naija News Hausa ta fahimci cewa, ‘yan kungiyar Biafra din sun bayyana rashin jin dadinsu ne bayan abin da ya faru a yadda wani Jami’in tsaro ya Harbe wani mai Babur a Aba.

4. Gwamnatin Jahar Zamfara ta Tsige Sarki, da Shugaban gunduma

Gwamnatin jihar Zamfara ta tsige Sarkin Maru, Alhaji Abubakar Cika Ibrahim da kuma shugaban gundumar Kanoma, Alhaji Ahmed Kanoma.

Naija News Hausa ta fahimci cewa an cire manyan shugabannin biyun ne a jihar bayan zargin kasancewa da liki da ‘yan fashi a yankin Jihar.

5. Sallah: Abin da Omo-Agege ya fadawa musulman Najeriya

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ovie Omo-Agege ya yi kira ga Musulmai da su yi amfani da lokacin Eid el-Kabir don yin addu’ar musanman ga kasar Najeriya.

Ya gargadi musulmai da su yi wa kasar addu’a domin shawo kan kalubalan da take fuskanta a yanzu.

6. Gobara ya kashe akalla Yara  a Takwa Bay, Jihar Legas

Mumunar Gobarar wuta ya kashe yara biyar a yankin Agbagbo, a Takwa Bay Island, a Jihar Legas.

Naija News Hausa ta fahimci cewa, rundunar ‘yan sandan jihar Legas ce ta yi wannan sanarwar a ranar Lahadin da ta gabata, a cikin wata sanarwa da aka bayyana Folake Ogundiya,‘ yar shekara 13, da kuma ‘yar uwanta’ yar shekara takwas, Abigail; dan shekara shida Daniel Bakare; Chidima Achomye, Nnamdi Achomye mai shekaru biyu da Khadijat da mutuwa a cikin hadarin.

7. Afenifere ta aika wa Shugaba Buhari Sakon Gargadi

Afenifere, wata kungiyar al’adar Yarabawan Najeriya, ta ce sukar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari, ya kasance ne saboda bukatar tabbatar da cewa gwamnatin na kan hanyar da ta dace.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a wata hira da Sakataren Jama’a yada yawun Afenifere, Yinka Odumakin, ya yi  da gidan Talabijin yada Labarai ta Channels TV.

Ka sami kari da Cikakken Labaran Najeriya a Hausa.NaijaNews.Com