Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Laraba, 14 ga Watan Agusta, Shekara ta 2019

Published

on

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Laraba, 14 ga Watan Agusta, 2019

1. El-Zakzaky Ya Isa kasar Indiya Don Binciken Lafiyar Jikin sa

Jagoran Kungiyar Harkar Musulunci a Najeriya (IMN), Sheik Ibrahim El-Zakzaky a ranar Talata ya sauka a Delhi, babban birnin kasar Indiya don neman karin lafiya.

Likitocin kasar Indiya sun karbe shi da kuma shigar da shi a cikin asibiti.

2. Shugaba Buhari ya baiwa Babban Banki CBN Sharadi Kan shigar da Abinci

Shugaba kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya bukaci Babban Bankin Najeriya (CBN) da daina ba da musayar kudin kasashen waje don shigo da abinci daga waje.

Naija News ta fahimci cewa an sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fito daga bakin mai magana da yawun shugaban kasa, Garba Shehu.

3. ‘Yan Jam’iyyar APC ne Kadai zan nada a cikin Karatuna – Oyetola

Gwamnan jihar Osun, Gboyega Oyetola ya bayyana cewa membobin jam’iyyar All Progressives Congress ne kawai za su yi zami jagoranci da wakilci a rukunin shugabancin sa.

Gov. Oyetola, a yayin da yake zantawa da manema labarai a Iragbiji, ya bayyana cewa duk da hakan ba zai yi watsi da ra’ayoyi daga ‘yan majalisar adawa ba, idan har zasu taimaka wa jihar ta zama da alheri.

4. Shugaban PDP Ya Bayyana Tallafi Ga RUGA Da Aka Kafa, tare da Dalilai

Babban jigon jam’iyyar Dimokradiyya, PDP, babbar Jam’iyyar adawar Najeriya, ya baiyana goyon baya ga kafa shirin karkara ta RUGA) da Gwamnatin Tarayya ta shirya da yi.

Naija News ta fahimci cewa Ciyaman, Kwamitin Amintattu (BOT) na PDP, Sen. Walid Jibrin ne ya sanar da hakan a ranar Talata da ta gabata.

5. Uwargidan tsohon Gwamnan Jihar Kwara ta musanta hada kai ga magudin kudi  Naira Biliyan N2bn

Lanre Bello, Babban Darakta na Leah Group ta mayar da martani game da wani labari da ake zargin ta dashi, mai cewa Uwargidan Tsohon Gwamnan Jihar Kwara na da halaka da cin hancin N2bn a asusun Kasuwancin kananan Hukumomi da Matsakaici (SMED).

Wannan ya bayyana ne kamar yadda wasu gidan labarai (ba da Naija News ba) suka yi jita-jitan cewa wata kila Hukumar Yaki da Cin Hanci da kare tattalin arzikin kasa (EFCC) zata kama Lanre akan zancen kudi Biliyan 2bn.

6. Gwmanan Jihar Legas, Sanwo-Olu mikar da jerin Ministocin Zuwa Ga Majalisar Dokoki ta Jiha

Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas a ranar Talata da ta wuce, ya mika jerin sunayen wadanda aka zaba domin nada ministocinsa ga majalisar dokokin jihar.

Naija News Hausa ta kula da cewa wannan Jerin itace na biyu bayana ‘yan makwanni hudu a baya da Gwamnan ya aikar da rukunin farko domin tantancewa.

7. Zargin Fyade: PFN na shirye Don Bada rahoto akan Fasto Biodun Fatoyinbo

Bayan zargin fyade da aka yi wa babban Fasto na Ikilisiyar CommonWealth of Zion Assembly (COZA), Biodun Fatoyinbo, kungiyar hadayyar Fentikostal ta Najeriya ta bayyana cewa za ta gabatar da rahotonta kan binciken zargin fyade a wannan makon.

Ka tuna cewa Hadadden kungiyar Kristocin Najeriya (CAN) ta baiwa PFN makwanni biyu don gabatar da rahoto kan zargin fyade da aka yiwa Fasto Biodun Fatoyinbo ta hannun Misis Busola Dakolo.

Ka samu kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com