IMN: Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya dage da kin Amincewa da Dokta da aka bayar don kula da shi | Naija News Hausa
Haɗa tare da mu

Labarai Hausa

IMN: Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya dage da kin Amincewa da Dokta da aka bayar don kula da shi

Published

Gwamnatin Kasar Indiya ta Gargadi El-Zakzaky don karaucewa ga ku binciken Jikin sa

Naija News Hausa ta karbi rahoto mai tabbaci a wata sako da aka wallafo a layin karban labarai ta mu, da cewa shugaban kungiyar ci gaban harkan musulunci ta Najeriya (IMN) wada aka fi sani da suna Shi’a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya ki karban kulawa daga likitoci da aka sanya don kula da shi.

Ko da shike an baiyana da cewa El-Zakzaky yayi hakan ne wai don bai san Likitocin ba, a bayanin an fada da cewa Likitocin sun bambanta da wadanda aka bayar daga Najeriya a ranar Litini kamin barin sa kasar zuwa Indiya.

Wani memba na Kungiyar Kare Hakkin Bil Adama ta IHRC da ya yi magana da manema labaran jaridar PRNigeria ta hanyar wani faifan sauti, ya ce gwamnatin Indiya a nunin halin tasu ya nuna El-Zakzaky a matsayin wani mugun dan ta’adda, “tun ma ba kotu a Najeriya da ta yanke masa hukunci zama dan ta’adda” inji shi.

Majiyar ta kara da cewa gwamnatin kasar Indiya ta baiwa El-zakzaky wa’adi na barin kasar Indiya idan har ya dage da kin karbar magani daga likitocin da aka sanya a yanzu don bashi kulawa.

KARANTA WANNAN KUMA; Eid El-Kabir: Kalli Bidiyon Aisha Buhari a Lokacin da ta ke Jifar Shaidan a Makka

 
Kuna iya aika Naija News ta hanyar amfani da maɓallin rabar mu. Aika duk labarai da sake bugawa zuwa [email protected].