Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litini, 19 ga Watan Agusta, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00
Manyan Labaran Jaridun Najeriya a Yau

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litini, 19 ga Watan Agusta, 2019

1. Farmaki ya tashi tsakanin Yarbawa da ‘Yan kasuwar Hausawa a jihar Legas

A ranar Lahadin da ta gabata, farmaki ya tashi tsakanin ‘Yan kasuwar Hausa da Yarbawa a kasuwar Oke-Odo da ke kan babbar hanyar Legas da Abeokuta.

Naija News bisa rahotanai ta gane da cewa wannan farmakin ya kai ga raunanar da mutum daya sosai, da kuma jawo katange babbar hanyar.

2. Shugabancin Kasar Najeriya ta yi Magana kan harin da IPOB tayi ga Ekweremadu

Ciyaman na kungiyar ‘yan Najeriya da ke a kasar Turai da kuma Mataimakiya na Musamman ga Shugaba Muhammadu Buhari kan al’amuran diflomasiya, Abike Dabiri-Erewa, ta yi Allah wadai da harin da a ka yiwa Sanata Ike Ekweremadu.

Naija News ta fahimci cewa an kai wa Ekweremadu hari ne a lokacin bikin al’adun gargajiya na shekara da shekara na kungiyar Ndigbo ta kudu maso gabas suka gudanar a Nuremberg, a kasar Jameni.

3. Dalili da ya sa Ziyara na ga Indiya ya zan da rashin Nasara – El-Zakzaky

Shugaban kungiyar Harkar Musulunci ta Najeriya (IMN), Ibrahim El-zakzaky, ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta nuna masa tsanancin gaske da rashin darajantawa lokacin ziyarar binciken lafiyar jikinsa a kasar Indiya.

El-Zakzaky ya bayyana hakan ne a wata faifan bidiyo, da cewa gwamnatin tarayya ta hana shi karban magani da bincike a asibiti.

4. Amurkawa ta la’anta Gwamnatin Shugaba Buhari a wata Sabon Rahoto

Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta bayyana cewa Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta gaza wajen samar da ci gaba a fagen bayyana kasafin kudin kasa.

Wannan bayani ya fito ne a wata zancen da rahoton Tarayyar Amurka na shekarar 2019 wanda ya gudana tsakanin watan Janairu 1 – zuwa Disamba 31, 2018.

5. Dalilin da yasa na ke son Odigie-Oyegun – Osinbajo

Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo a ranar Asabar din da ya gabata ya bayyana dalilai biyu da suka sa ya ke girmama da son tsohon Shugaban Jam’iyyar APC ta tarayyar Najeriya, John Odigie-Oyegun.

Ya sanar da hakan ne yayin da yake jawabi wajen bikin cikar shekaru 80 ga haifuwa na Oyegun, tsohon gwamnan jihar Edo, a Abuja.

6. Nnamdi Kanu a karshe ya yada yawu bayan harin da IPOB suka yi wa Ekweremadu

Jagoran ‘Yan asalin yankin Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu, ya mayar da martani kan harin da aka kaiwa tsohon mataimakin shugaban majalisar dattijai, Sanata Ike Ekweremadu, a Nuremberg Jamus.

Naija News ta ruwaito tun da farko cewa membobin kungiyar IPOB sun kai wa Ekweremadu hari a yankin Nuremberg, ta kasar Jamus a ranar Asabar, 17 ga Agusta da ta gabata.

7. JAMB ta sanar da sabon gargadi ga Dalibai da sabon Tsarin neman shiga Jami’a Babba

Hadaddiiyar Hukumar Gudanar da Jarabawan shiga Jami’a babba, JAMB ta shawarci masu neman shiga babban Makarantar Jami’a da ke shirin jarabawan (UTME) da su din ga karanta kuma bin umarnin da ke kunshe a cikin takaddar gwaji kafin yin rajista.

JAMB ta sanar da hakan ne ta bakin Shugaban Sadarwa da Yada yawun hukumar, Mista Fabian Benjamin, a yayin wata tattaunawa da yayi da Kamfanin Dillancin Labarai na NAN a ranar Asabar a Abuja.

8. Abinda Fayose ya fada Bayan da Wakilan Kungiyar IPOB suka kaiwa Ekweremadu hari

Tsohon gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose ya la’anci harin da aka kaiwa tsohon mataimakin shugaban majalisar dattijai, Ike Ekweremadu, da wasu mambobin kungiyar ‘yan asalin yankin Biafra (IPOB) suka yi masa.

Naija News ta ruwaito tun da farko cewa membobin kungiyar IPOB sun kai hari ga Ekweremadu a Nuremberg, Jamus a ranar Asabar, 17 ga Agusta.

Ka sami kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa