Connect with us

Uncategorized

NYSC: Yadda Hadarin Mota ya tafi da rayukar wasu ‘Yan Bautan kasa a Katsina

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wasu Matasa Uku da ke hidimar Bautan Kasa (NYSC), a cikin jihar Katsina sun mutu a yayin da wasu goma sha daya suka sami raunuka daban-daban a wani hadarin babur da ya faru a safiyar ranar Lahadi da ta gabata.

Naija News Hausa bisa rahotannai da ta gane da shi, an sanar da cewa ‘yan Bautan Kasar suna kan tafiya ne a cikin wata Motar Toyota Bus dauke da lambar rajista: MAN 45 AA, ta Kungiyar ‘yan Bautan kasa na Ikilisiyar Katolika, watau National Association of Catholic Corps Members (NACC), daga garin Katsina zuwa karamar hukumar Funtua don hallatar wata hidimar daurin aure.

Hadarin da ya faru a kauyen Gobirawa a cikin garin Kankara, sanadiyar mumunar yawar gudu ne da kuma rasa mafita. inji kakakin yada yawun hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC), Abdullahi Danladi, wanda ya tabbatar da hadarin ga manema labarai.

Gwamnan jihar, Aminu Masari, wanda shi ma ke kan tafiya a kan hanyar a lokacin da hatsarin ya faru, ya bada umarni an kwase gawarwakin tare da masu raunuka a cikin motar da ke biye da shi.

Ko da shi ke har yanzu ba a iya gane fuskar wadanda suka yi hadarin motar ba tukuna.

KARANTA WANNAN KUMA: Shahararren Jigo, Adam A. Zango ya fita daga Kannywood