Gwamnatin Jihar Kano ta Shirya da bayar da Daji Biyar ga Makiyaya don aikin Kiwo a Jihar | Naija News Hausa
Haɗa tare da mu

Labaran Siyasa

Gwamnatin Jihar Kano ta Shirya da bayar da Daji Biyar ga Makiyaya don aikin Kiwo a Jihar

Published

Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana da shirin sauya daji biyar zuwa ga makiyaya Fulani a jihar don samun wajen kiwon dabobin su.
Naija News Hausa ta samu tabbacin hakan ne bisa wata sanarwa da Gwamna Abdullahi Ganduje, Gwamnan Jihar Kano ya sanar a ranar Talata da ta gabata yayin da yake zantawa da manema labarai a birnin Tarayya, Abuja.

Gwamna Ganduje ya bayyana cewa gwamnatin sa ta kaddamar da kwamitin kwararru kan mazauna karkatar makiyaya a jihar. Ya kuma kara da cewa, shirin da aka gabatar zai taimaka matuka ga jihar wajen bunkasa ayyukan ci gaban tattalin arziki a jihar.

Ya kara da bada hasken cewa shiri zai kuma hana da magance tafiye-tafiyen makiyaya, musanman barin Arewa zuwa Kudu, da sauya tsaguni da tashin hankali da ke faruwa tsakanin Makiyaya da Mazauna yankin Kudun kasar.

Ganduje ya kara da cewa zai samar da kayan zaman Al’uma kamar su Asibiti, Asibitin kula da Lafiyar Dabobi, Kasuwa, Tsaro da Makarantu ga Makiyayan don su ma su ci amfanin arzikin kasar kamar yadda take alhakin kowani dan Najeriya.

A cewarsa, “bai dace a ce Gwamnatin Tarayya ne ke sasantawar makiyaya ba kawai, yakamata ya kasance batu da hidimar jiha ne saboda suna rayuwar su da bunkasa ne a kowane yanki” inji Ganduje.

“Gwamnati na za ta sake yin kokarin da take tun a da don ganin cewa manoma sun ji dadin hidimomin tallafi da ayyukan bunkasa noma a jihar Kano.”

 
Kuna iya raba Naija News ta hanyar amfani da maɓallin raba mu. Aika duk labarai da sake bugawa zuwa newsroom@naijanews.com.