Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Alhamis, 22 ga Watan Agusta, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Alhamis, 22 ga Watan Agusta, 2019

1. Buhari Ya Sanya wa sabbin Ministocin ‘Matsayi

A ranar Laraba da ta gabata, Shugaba Muhammadu Buhari ya ba da takardu Matsayi ga sabbin Ministocin da aka rantsar a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.

Naija News ta tuno da cewa Buhari ya nada mutum 43 a matsayin ministocin da za su taimaka masa a wasu mukamai daban-daban a mulkinsa na karo biyu bayan hutun hidimar ilimantar da su kwana biyu.

2. Ku yi Watsi da Zancen PDP na Neman Takarda na, Babu wata doka da ta bukace Ni da gabatar da hakan – inji Buhari

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a ranar Laraba da ta wuce ya bukaci Kotun daukaka kara ta Shugaban kasa da ke zaune a Abuja don yin watsi da takaddamar da Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP ya ke yi.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa babu wata doka a Najeriya da ta bukace shi da ya bayarda takardar sa ta tabbatar da cancantarsa ​​ta neman shugabancin kasar.

3. Nnamdi Kanu yayi Magana kan wasikar Gwamnonin Kudu Maso Gabas Ga shugaba Buhari

Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar ‘Yan asalin yankin Biafra ya mayar da martani ga wasikar da Gwamnonin Kudu maso Gabas suka aika wa Shugaba Muhammadu Buhari.

Ku tuna Naija News ta ruwaito a baya da cewa gwamnoni daga yankin kudu maso gabas sun aika wa Shugaba Buhari wasika a kan rufe filin jirgin saman Akanu Ibiam da kuma harin da wasu Makiyaya suka kai wa mutanen yankin a kwanan nan.

4. APC Za Ta Kare kan Shugabancin Buhari A Shekarar 2023 – Shehu Sani

Tsohon Sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana cewa shugabancin Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) zai kare ne da zarar Shugaba Muhammadu Buhari ya kammala wa’adin nasa a 2023.

Shehu ya bayyana cewa ba a kafa jam’iyyar APC ba da hangen gaba da manufan kwarai, saboda haka za ta kare a shekarar 2023.

5. Atiku ya ɓata lokacinmu ne kawai – INEC

Hukumar Gudanar da Hidimar Zaben Kasar Najeriya, INEC ta bukaci kotun daukaka karar neman takarar shugaban kasa da ta yi watsi da karar da ta shigar ta hannun Atiku Abubakar da tawagarsa.

Kungiyar zaben ta kara da cewa karar da Atiku da Jam’iyyar Dimokradiyya ta gabatar na kalubalantar nasarar Shugaba Muhammadu Buhari da Jam’iyyar All Progressives Congress a zaben shugaban kasar da aka yi ranar 23 ga watan Fabrairu a Najeriya babban koma-baya ne da batar da lokaci ga kotun.

6. Shugaba Buhari ya rantsar da Ministocin Next Level

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba da ta gabata, ya kaddamar da hidimar rantsar da mutane 43 a matsayin ministocin da za su taimaka masa a wasu mukamai daban-daban a lokacin mulkinsa na karo biyu.

Kamar yadda Naija News ta ruwaito a baya, da cewa Shugaban zai nada mukamai ga ministocin bayan bikin rantsuwar kamar yadda aka tabbatar a cikin wata sanarwa da Femi Adesina, mai ba da shawara na musamman ga shugaban kasa kan shafin yada labarai ya bayar.

7. Ban san Yadda Ma’aikatata take gudana ba – Aregbesola

Rauf Aregbesola, sabon Ministan Aikace-aikacen Gida a Najeriya, ya ce bashi da masaniyar yadda ma’aikatar ke gudanar da ayyukan ta.

Naija News ta fahimci cewa Aregbesola ya yi wannan bayanin ne lokacin da ya ziyarci ma’aikatar harkokin cikin gida jim kadan bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya rantsar da shi.

8. ‘Yan Hari da Bindiga sun kai hari ga Mataimakin Gwamnan Nasarawa, da kuma Kashe Mutane Hudu

Wasu Mahara da Bindiga a ranar Talata da ta wuce sun kai hari a tawagar Mataimakin Gwamnan Jihar Nasarawa, Emmanuel Akabe, inda suka kashe ‘yan sanda uku da wani direba.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa Mataimakin gwamnan yana kan hanyarsa ta zuwa Abuja ne a lokacin da shi da tawagarsa suka fada a hannun ‘yan bindigar, a ‘yan kilomita kadan daga Akwanga a Nasarawa da misalin karfe 6 na yamma.

9. Abin da Shugaba Buhari ya ce a yayin rantsar da ministoci

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a ranar Laraba da ta gabata yayi bayani a yayin rantsar da mutane 43 a matsayin ministocin da za su taimaka masa a sashe daban-daban a lokacin wa’adinsa na biyu a kan mulki.

Naija News ta tunatar da cewa kafin bikin rantsar da Ministocin a ranar Laraba, majalisar dattijai ta yi bincike da tantance Ministocin bisa ga jerin sunayen da Shugaba Buhari ya mikar ga Majalisar a kwanakin baya.

Ka sami kari da cikakken Labaran a shafin NaijaNewsHausa