Sabuwar Labari: 'Yan Hari sun Sace Dan Majalisa, Aminu Magaji a Jihar Sakkwato | Naija News Hausa
Haɗa tare da mu

Labaran Siyasa

Sabuwar Labari: ‘Yan Hari sun Sace Dan Majalisa, Aminu Magaji a Jihar Sakkwato

Published

Naija News Hausa ta karbi sabuwar rahoton cewa wasu Mahara da Bindiga da ba a gane da su ba sun sace wani dan majalisa a jihar Sakkwato. A halin yanzu wannan al’amarin ya riga ya tayar da hankalin mazauna yankin.

Bisa rahoton da manema labaran jaridar Punch suka bayar, An sace Aminu Magaji Bodai, wakilin da ke wakiltar mazabar Denge / Shuni a majalisar dokokin jihar Sakkwato ne, da safiyar ranar Alhamis.

Don kara bada tabbaci ga al’amarin, wani dan uwa ga dan Majalisar ya bayyana ga manema labarai da cewa an sace Aminu ne a misalin karfe 1:15 ta safiyar ranar Alhami, yau, a tsakanin kauyan Dange da Bodai.

“Ina iya tabbatar muku cewa mutanen da ba a sansu ba sun sace dan’uwana a yau. Har yanzu ba a san inda yake ba kuma wadanda suka sace shi har yanzu ba su yi magana da ko mutum daya a cikin danginsa ba” inji bayanin dan Uwa ga Dan Majalisar.

A lokacin da aka tuntube rundaunar ‘yan sandan jihar, shugaban Jami’an tsaron PPRO Mohammed Sadiq Abubakar ya bayyana da tabbacin al’amarin, ko da shike a ya kara da cewa a halin sun bincike a yayin da ba cikakken ganewa da harin.

Ka tuna da cewa Naija News Hausa ta ruwaito a baya cewa ‘Yan Hari da Makami sun kashe Mutane Hudu a wata Sabuwar Hari a Jihar Katsina.

 
Kuna iya raba Naija News ta hanyar amfani da maɓallin raba mu. Aika duk labarai da sake bugawa zuwa newsroom@naijanews.com.