Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata 27 ga Watan Agusta, Shekara ta 2019

Published

on

at

Listen to article
0:00 / 0:00

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Talata 27 ga Watan Agusta, 2019

1. Shugaban Kasa Buhari ya sauka a Kasar Japan duk da Matsalolin da ke gudana

Duk da jita-jitar da ke gudana game da wani shirin zanga-zangar da mambobin kungiyar ‘Yan Asalin Biafra (IPOB) suka yi, Shugaba Muhammadu Buhari ya isa kasar Japan a ranar Litinin.

Naija News ta fahimta da cewa shugaban kasar ya tafi kasar Japan ne don halartar Taron kasa da kasa ta karo 7 ne a Tokyo kan cigaban Afirka wanda aka gudanar a Garin Yokohama daga ranar 28 ga Agusta zuwa 30 ga Agusta.

2. Gwamnatin Jihar Kaduna Sun Bayyana Shirin Fara Biyan Sabuwar Albashin Ma’aikata

Gwamnatin gwamna Nasir El-Rufai ta jihar Kaduna a ranar Litinin ta sanar da cewa za ta fara biyan sabon mafi karancin albashi na ma’aikata daga ranar 1 ga Satumba, 2019.

Gwamnatin jihar ta sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa da mai ba da shawara na musamman ga gwamna El-Rufai kan harkokin yada labarai da sadarwa, Muyiwa Adekeye, ya bayar.

3. Kotu Karar Shugaban kasa ta sanya ranar yanke hukunci ta karshe

Kotun sauraron karar shugaban kasa ta gabatar da ranar 13 ga Satumbar, 2019, don yanke hukunci kan karar da Atiku Abubakar ya yi wa Shugaba Muhammadu Buhari.

Naija News ta fahimci cewa, Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Babban Jam’iyyar Adawar kasar Najeriya, na kalubalantar sakamakon zaben ranar 23 ga watan Fabrairu wanda hukumar zaben ta bayyana Shugaba Buhari a matsayin wanda ya lashe zaben.

4. Boko Haram: Mazauna Borno Sun Wallafa wata Wasika ga Shugaba Buhari

Mazauna jihar Borno sun fada wa Shugaba Muhammadu Buhari da cewa ba a shawo kan matsalar ‘yan kungiyar ta’adda ba, watau Boko Haram, kamar yadda ake zantarwa a labarai da cewa an ci nasara da ‘yan ta’addar.

Mazauna yankin sun kuma kara da bayyana cewa mazauna yankin suna cikin fargaba ko da yaushe, musanman sauraron ko ta ina ne hari zai taso a nan gaba.

5. EFCC: Atiku ya Bayyana Dalilin da yasa Ya Ba da Miliyan 50 ga dakin karatun Obasanjo

Tsohon Mataimakin Shugaban Najeriya da kuma dan takarar Shugaban kasa a zaben 2019 na Jam’iyyar Peoples Democratic Party, Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana dalilin da ya sa ya bayar da tallafin Naira miliyan hamsin ga dakin karatun tsohon Shugaban Kasa, Olusegun Obasanjo.

A yayin da yake bayyana dalilin da ya sa ya ba da irin wannan kudin ga dakin karatu na tsohon shugaban kasar, a ranar Litini ya fada da cewa kudin kyauta ne kawai.

6. Wike ya musanta zancen Rushe Masallacin Central-Amadi

Gwamnan jihar Rivers, Mista Nyesome Wike ya musanta zancen cewa ya rushe Masallacin Central ta Masadi.

Da yake zantawa da manema labarai da safiyar yau a kan hanyar Titin Biambo, ta hanyar Makarantar da ke kusa da Kasuwar Mami, ya ce lallai babu Masallaci a gine a wurin, saboda haka babu abin da aka rushe.

7. Kotu ta yi kira ga Hukumar EFCC da AGF akan Mallakar Yari

Babban Kotun Koli da ke a birnin Abuaja ta yi kira ga Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da kuma kare Tattalin Arziki Kasa (EFCC) da babban Alkalin Tarayyar kasar Najeriya (AGF), Abubakar Malami, da su bayyana a gaban kotun akan zancen gurfanarwa da shirin kwace Mallakar Abdulaziz Yari, tsohon gwamnan jihar Zamfara.

Naija News ta fahimta da cewa kotun ta gayyaci hukumar EFCC da AGF ne a ranar Litinin ne.

8. Gwamna Ishaku yayi Magana Akan Bai wa Wadume Miliyan N6m don hidimar zabe 2019

Gwamnan jihar Taraba, Darius Ishaku ya karyata alaƙa da sanannen shugaban ‘yan Fashi da aka kame, Hamisu Bala, wanda aka fi sani da Wadume.

Gwamnan ya karyace zancen cewa ya baya da Naira miliyan shida ga Wadume don hidimar zaben shekarar 2019 da aka kamala a baya a Jihar.

Ka sami kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com