Connect with us

Labaran Najeriya

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Laraba 28 ga Watan Agusta, Shekara ta 2019

Published

on

at

advertisement

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Laraba 28 ga Watan Agusta, 2019

1. Buhari ya Umurci EFCC, NIA don Binciken kwangilar 2010

Shugaban hukumar tattalin arziki kasa da yaki da cin hanci da rashawa, tare da hukumar leken asirin kasa da kuma Insfekta Janar na ‘yan sanda, sun karbi umarni daga shugaban kasa Muhammadu Buhari da su binciki tsari da ci gaban Masana’antu wanda a kwanan nan suka sami umarnin kotu a Burtaniya don kwace Tattali da Arzikin Najeriya mai kimanin kudi dala biliyan $9.6.

An sanar da hakan ne a bakin Ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed, a wani taron manema labarai a Abuja ranar Talata da ta gabata.

2. Majalisar dokokin jihar Legas ta fara bincike kan Gwamnatin Ambode

Majalisar dokokin jihar Legas ta fara bincike game ayuka da tafiyarwa na tsohon gwamnan Jihar Legas, Akinwunmi Ambode.

Naija News ta fahimci cewa Majalisar ta kafa kwamiti wanda Hon. Fatai Mojeed zai jagoranta don binciken sayan motocin bas 820 domin jigilar jama’a a jihar da aka yi a lokacin shugabancin gwamna Ambode.

3. Shugaba Buhari ya tisge Shugaban Hukumar Kula da Mahajjata ta Kirista

A ranar Talata da ta gabata, shugaba Muhammadu Buhari ya tsige Sakataren zartarwa na Hukumar Kula da Mahajjata ta Kiristocin Najeriya, Rev Tor Ujah.

An sanar da wannan ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Daraktan yada labarai, ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya, Willie, Bassey, a madadin SGF, Boss Mustapha.

4. ‘Yan Kungiyar IPOB Sun yi zanga zangar bukatar kame Shugaba Buhari a Kasar Japan

Mambobin kungiyar ‘yan asalin yankin Biafra (IPOB) a ranar Talata da ta gabata, sun gudanar da wata zanga-zangar neman kama Shugaba Muhammadu Buhari a Japan.

Masu zanga-zangar sun isa gidan jakadan Najeriya a Japan da sanyin safiyar ranar Talata, suna masu cewa suna hari wajen ne don yin gwajin jinin Shugaba Buhari.

5. Duba Dalilin da yasa Najeriya zasu Biya karin kudi Visa ta shiga Amurka

Ofishin jakadancin Amurka ta bayyana cewa ‘yan Najeriya za su kara ga biyan kudin takardan Visa na shiga Amurka.

A cewar Ofishin jakadancin na Amurka, karin kudin ya kasance ne bisa karin kudin visa da gwamnatin Najeriya ke karba a hannun ‘yan Amurka.

6. Zagin Fyade: ‘Yan sanda sun binciki Fasto Fatoyinbo A CID, Abuja

Babban Fasto na Ikilisiyar COZA da ke da Hedikwatarta a birnin Abuja, Biodun Fatoyinbo, a yanzu haka yana fuskantar tambayoyi da bincike a hedikwatar rundunar ‘yan sanda ta CID da ke Abuja kan zargin fyade da matar Timi Dakolo, Busola Dakolo ta yi masa.

Shahararren mai daukar hoton ta zargi faston COZA da yi mata fyade shekaru 20 da suka gabata, kamin tayi aure da Timi Dakolo, shahararren mawaki a Najeriya.

7. Sabuwar Kanancin Albashi: NLC ta Gargadi Gwamnatin Buhari

Kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC) ta gargadi gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari kan kara bata lokaci ga aiwatar da sabon matakin mafi karancin albashi na kasa.

Kungiyar kwadagon ta sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa da aka bayar a hannun shugaban, Ayuba Wabba da kuma babban sakataren kungiyar Peter Ozo-Eson, taron majalisar zartarwa ta kasa (NEC).

8. Duba Jami’an ‘Yan Sanda da ake zancen tsigewa domin Taimakawa Wadume da Gudun Hijira

Bincike da bayanai na nuna cewa za a tsige ‘yan sanda da ake zargi da taimakawa da tserewar shugaban ‘yan fashi da aka kame kwanakin baya, Hamisu Bala, da aka fi sani da suna Wadume.

Bayanai da Naija News ta tattara ya nuna da cewa wasu ‘yan sanda biyu sun hada hannu da Wadume don tabbatar da tserewarsa.

Karanta kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin NaijaNewsHausa